Jose Mourinho ne ya fara daukar dukkan kofunan Zakarun Turai

Jose Mourinho ya zama na farko da ya lashe sabon kofin gasar Turai da ake kira da Conference League ranar Laraba.

Roma ta lashe kofin ne, bayan da ta yi nasara a kan Feyenoord Rotterdam da ci 1-0, kuma Nicolo Zaniolo ne zura kwallon a raga a minti na 32 a karawar da suka yi a Albania.

Da wannan nasarar dan kasar Portugal ya zama na farko da ya ci dukkan kofunan gasar Zakarun Turai a tarihinsa na horar da tamaula.

Mourinho ya lashe wasan karshe karo biyar da ya je fafatawar karshe a gasar Zakarun Turai, shi ne kan gaba a wannan bajintar.

Jerin kofunan da Mourinho ya lashe a gasar Zakarun Turai:

Kungiya Kakar tamauala Kofin da ya dauka

Porto 2002-03 Uefa Cup

Porto 2003-04 Champions League

Inter Milan 2009-10 Champions League

Manchester United 2016-17 Europa League

Roma 2021-22 Europa Conference League

Wannan shi ne kofi na 26 da Mourinho ya dauka a tarihin horar da tamaula - shekara 19 bayan da ya dauki Uefa Cup a 2003 a Porto.

A watan Mayun bara aka nada shi kociyan Roma, wanda aka bai wa alhakin gina kungiyar da bunkasa ta, bayan da ta karkare a mataki na bakwai a Serie A ta kakar 2020-21.