Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko cinikin 'yan kwallo a bana zai yi armashi kuwa?
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Cikin watan Agusta za a fara kakar tamaula a wasu kasashe a nahiyar Turai, tuni wasu kungiyoyin suka yi nisa wajen daukar 'yan wasan da za su taka musu rawar gani a kakar 2021-22.
Hakan ne ya sa wasu kungoyin ke zawarcin 'yan kwallon da suka taka rawar gani a Euro 2020 da wadanda suka yi bajinta a Copa America a bana,
To sai dai kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta bana ta ci karo da koma bayan da cutar korana ta haddasa na karancin kudi tun daga kakar bara.
Za ka iya fahimtar hakan cewar kungiyoyi da dama na son kara karfinsu don tunkarar kalubalen gasa mai zuwa, amma ba kudi a kasa, sun gwammace su karbi aron dan wasa ko daukar wadanda kwantiraginsa ya kare,
Kawo yanzu RB Leipiz ce kan gaba wajen hada-hada mai tsoka da ta kai sama da Yuro miliyan 91, wadda ta dauki Andre Silva kan Yuro miliyan 23 daga Eintracht Frankfurt.
Haka kuma kungiyar ta Jamus ta sayar da Dayot Upamecano ga Bayern Munich kan Yuro miliyan 42.5 da kuma Ibrahima Konate ga Liverpool da ake cewar kudin cinikin ya kai Yuro miliyan 40.
Idan ka auna karfin tattalin Paris Saint-Germain, amma ta amince ta dauki Sergio Ramos da kuma Gianluigi Donnarumma, wadanda yarjejeniyarsu ya kare a kungiyoyinsu har da Georginio Wijnaldum daga Liverpool.
Itama Barcelona 'yan kwallo uku ta dauka a bana wadanda kwantiraginsu ya karkare a kungiyoyinsu ciki sun hada da Sergio Aguero da Eric Garcia da kuma Memphis Depay.
Kawo yanzu Manchester United ce kan gaba da ta dauki dan wasa daya da tsada, shine Jadon Sancho daga Borrusia Dortmund, amma dai za a iya fahimtar yadda cutar korana ta durkusar da cinikin 'yan kwallo a bana kamar yadda ya faru a bara.
Kungiyoyi da dama sun zabi su dauki aron dan wasa maimakon su mallake shi, sannan wasu na ta kokarin ganin wadanda suke karbar albashi mai tsoka sun rage zuwa wani kaso duk don tsuke bakin aljihu.
Wannan koma bayan ya ci karo da cutar korna da ta haddasa, ciki har da yin wasanni ba 'yan kallo a sitadiya da sauransu tun daga bara.
Sai dai ana sa ran magoya baya za su koma kallon wasanni ido da ido cikin kakar da za a fara a wasu manyan kasashen Turai daga watan Agusta, wanda hakan zai farfado da wasu abubuwan da aka hakura da su a fannin kwallon kafa, sakamakon bullar Annobar,