Real Madrid 0-4 Barcelona: Barca ta hada maki uku a Bernabeu

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta doke Real Madrid 4-0 a wasan mako na 29 a gasar La Liga da suka kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.
Pierre-Emerick Aubameyang ne ya fara cin kwallo, sai Ronald Araujo ya kara na biyu sannan suka je hutun rabin lokaci,
Bayan da suka koma wasan zagaye na biyu ne Ferran Torres ya kara na uku, daga baya Pierre-Emerick Aubameyang ya ci na hudu, kuma na biyu da ya zura a raga a wasan farko da ya buga a El Clasico.
Aubameyang ya ci kwallo tara a karawa 11 da ya yi wa Barcelona tun bayan da ya koma Camp Nou a watan Fabrairu daga Arsenal a matakin wanda bai da kwantiragi.
Da wannan sakamakon Barcelona ta yi wasa 12 a jere ba tare da an doke ta ba, sannan ta kawo karshen fafatawa 11 da Real Madrid ta yi ba tare da an yi nasara a kanta ba.
Kungiyoyin biyu sun hadu sau biyu a bana kafin ranar Lahadi, inda Real Madrid ta ci 3-2 a Spanish Super Cup a Saudi Arabia ranar 12 ga watan Janairun 2022.
Kafin nan Barcelona ta yi rashin nasara da ci 2-1 a Camp nou a gasar La Liga ranar 24 ga watan Oktoban 2021.
Real Madrid tana mataki na daya da maki 66 a kan teburin La Liga a kakar nan da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona mai kwantan wasa mai maki 54 ta uku a teburin.
Benzema bai samu damar fuskantar Barcelona ba, wadda itace ta hudu a jerin kungiyoyin idan ya hadu da su sai ya ci kwallo mai 11 a raga, ya kuma bayar da 10 aka ci Barcelona a karawar da ya yi da ita.
Benzema shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga ta bana mai 22 kawo yanzu, sai Enes Unal na Getafe da Vinicius Junior na Real Madrid da kowanne keda 14 a raga.
'Yan wasan Real Madrid da suka fuskanci Barca:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Diego.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco, Camavinga.
Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.
'Yan wasan Barcelona da suka fafata da Real Madrid:
Ter Stegen, Piqué, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Memphis, Adama da kuma Braithwaite.
Sauran sun hada da Neto, Nico, Lenglet, Pedri, L. De Jong, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Gavi and Arnau Tenas.
Wadanda ke jinya a Barcelona kawo yanzu sun hada da Dest, Ansu Fati, Sergi Roberto da kuma Samuel Umtiti.











