Karim Benzema ne kashin bayan Real Madrid a bana

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Lahadi Real Madrid ta yi rashin nasara a wasan farko a La Liga a bana, bayan da Espanyol ta doke ta 2-1.

Karim Benzema ne ya ci wa Real kwallon a wasan mako na takwas, koda yake har yanzu ita ce ta daya a kan teburi da maki 16 iri daya da na Atletico Madrida ta biyu.

Kawo yanzu dan wasan tawagar Faransa ya ci kwallo 10 a Real Madrid jumulla, duk da baya samun mataimaka sosai a fafatawar da yake yi.

Wani lokacin shine yake karbo kwallon da zai zura a raga, bayan tare da yake yi a lokacin da masu tsaron bayan Real Madrid keda rauni da za a iya cin kungiyar daga ko ina.

Ko a wasan Champions League da ta buga ranar Talat 28 ga watan Satumaba, FC Sheriff Tiraspol ce ta je ta doke Real da ci 2-1, kuma Benzema ne ya ci mata kwallo tilo a karawar.

Kawo yanzu Benzema mai kwallo 10 da ya ci wa Real kawo yanzu, tara daga ciki a La Liga ya zura a raga, sannan ya bayar da bakwai aka ci, kenan yana da hannu a 16 daga 22 da kungiyar ta zazzaga a raga kawo yanzu.

Dukka da cewar Benzema ya fara kakar bana da kafar dama, bayan wasa takwas da ya buga wa kungiyar a La Liga, ba lalle bane ya ci gaba da kokari haka har kammala kakar nan, kuma dan wasa baya rabuwa da rauni da yin jinya.

Wanda ke taimakawa Benzema shine Vinicius, wanda shima ya fara kakar bana da abin azo a gani, wanda mako biyu da ya wuce ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a karawar da Real ta yi nasara a kan Valencia.

Kawo yanzu dan kwallon tawagar Brazil ya ci biyar ya kuma bayar da biyu aka zura a raga ya kuma yi sanadin samun fenariti biyu da Benzema ya buga ya ci.