Arsenal 'ba za ta sayar' da Emily Smith Rowe ga Aston Villa ba

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ba ta da shirin sayar da Emile Smith Rowe ga Aston Villa a karshen kakar bana in ji Mikel Arteta.
Villa ta tuntubi Gunners kan ko za a sayar mata da matashin dan kwallon kafar tawagar Ingila a karshen kakar nan.
Wasu rahotanni daga jaridun Burtaniya sun wallafa cewar sau biyu Villa na taya Smith Rowe tun kan fara kakar bana, amma Gunners taki sallamarwa.
Tuni kuma dan wasan mai shekara 20 ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo ta ci gaba da taka leda a Arsenal, inda ya kawo karshen rade-radin da ake yi kan makomarsa a kungiyar.
Dan wasan da ya fara Arsenal tun yana da shekara tara ya zama kashin bayan kungiyar a bara, wanda ya buga wasa 30 da cin kwallo uku ya kuma bayar da biyar aka zura a raga.
Arsenal tana mataki na 12 a teburin Premier League da maki 10, ita kuwa Villa tana ta 13 mai tazarar maki daya tsakaninta da Gunners.
Ranar Juma'a Arsenal za ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan mako na tara a gasar Premier League.







