Arsenal: Mikel Arteta na bukatar lokaci a ƙungiyar - Danny Murphy

Mikel Arteta

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Mikel Arteta ya fara jan ragamar Arsenal a 2019

La'akari da yadda salon wasan Arsenal ke tabarbarewa a 'yan makonnin da suka wuce, za'a iya cewa sakamakon da ta samu a gidan Leeds United na 0-0 tare da samu jan kati ya yi mata kyau.

To sai dai sakamakon ya biyo bayan kashin da Arsenal ta sha har gida na 3-0 a hannun Aston Villa mako biyu da suka wuce.

Hakan ya sa Arteta ke ci gaba da fuskantar matsin lamba, don a yanzu kungiyar na matsayi na 11 a teburin Premier, bayan lashe wasa daya a cikin biyar.

Abin da ya fi damun magoya baya ma shi ne rashin cin kwallaye da kungiyar ke fama da shi, kuma hakan ya sa suke ganin akwai inda baraka take.

Amma masu fashin baki kamar tsohon dan wasan Ingila Danny Murphy, na ganin cewa gajen hakuri ne a ce kungiyar ta fara ganin laifin Arteta, don kuwa salon wasansa na da kyau, abin da kawai yake bukata shi ne a ba shi lokaci.

A cewar Murphy yana da kwarin gwiwar cewa Mikel Arteta zai sauya al'amura a Arsenal.

Masu fashin baki sun nuna gamsuwa da salon wasan Mikel Arteta
Bayanan hoto, Masu fashin baki sun nuna gamsuwa da salon wasan Mikel Arteta

Ya ce: 'Ina ganin rashin adalci ne a ce har an fara ganin laifin Arteta lura da yadda kungiyoyi kamar Manchester United da Manchester City suka gaza yin abin da ya yi kawo yanzu'.

"Da farko wasan ya karbe shi, 'yan makonnin da suka wuce ne ake samun kwan-gaba-kwan-baya a kungiyar, amma ina da kwarin gwiwa zai sauya al'amura idan aka ba shi lokaci'.

Arsenal ta kare wasanta na ranar Lahadi a gidan Leeds United 0-0, kuma dan wasanta Nicolas Pepe ya samu jan kati.

Hakan ya sa ta hada maki 13 a wasa tara, kuma take a mataki na 11 a kan teburin Premier.

Arsenal na zaune a na 11 kan teburin Firimiya bayan lashe wasa daya a cikin biyar
Bayanan hoto, Arsenal na mataki na 11 kan teburin Premier bayan lashe wasa daya a cikin biyar