Karsashin Lionel Messi ya koma ga tawagar Argentina

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin Lionel Messi na daf da jan ragamar Argentina zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
A baya can za a iya fuskantar farincikin Messi a wasannin da ya buga wa tsohuwar kungiyarsa Barcelona da kwazon da yake yi, wanda ake zarginsa da cewar baya sa kwazon da ya kamata a tawagar Argentina.
To sai dai kuma wannan batun ya kau a wannan lokacin da kowa ya fahimci yadda Messi ke jin dadin buga wa tawagar Argentina wasanni da kuma karsashin da yake ji a wannan lokacin.
Tun bayan da Messi ya bar Barcelona a bana ya koma Paris St Germain da taka leda wani nauyi ya sauka a kansa da cewar sai ya yi bajinta a kungiyar Sifaniya.
Yanzu nauyi daya ne ke kansa shine a tawagar Argentina, wadda ya ja ragamar lashe Copa America a bana, bayan doke Brazil 1-0 a watan Yuli.
Hakan ya kawo karshen gori da ake masa cewar bai taba lashe babban kofi a babbar tawagar Argentina ba.
A yanzu baya fuskantar kalubale a sabuwar kungiyarsa ta PSG wadda ya ci mata kwallo daya kawo yanzu shine da ya zura daya a ragar Manchester City a Champions League.
Dan wasan ya mayar da hankali wajen kai Argentina gasar cin kofin duniya da za a yi a 2022 a Qatar, kuma watakila babbar gasar da zai je kenan ta karshe yana da shekara 25 a lokacin.
Messi ya fuskanci kalubale a wasannin Argentina, wanda ta kai ya yi ritaya daga buga mata tamaula, bayan da ake kwatanta nasarar da ya samu a Barcelona.
Daga baya aka rarrashe shi ya dawo ci gaba da buga mata tamaula, wanda ta kai da ya daga Copa America a bana, yana kuma sa ran kai ta gasar kofin duniya a badi.
A karshen mako Messi ya ci Urugay kwallo a 3-0 da Argentina ta yi nasara a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya shiyyar Kudancin Amurka,
Kwallon da Messi ya ci ita ce ta 80 jumulla, kuma shine kan gaba a yawan cin kwallaye a Kudancin Amurka.
Kawo yanzu Argentina tana mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Brazil ta daya a teburin da kasashe hudu ke wakiltar Kudancin Amurka kai tsaye a gasar kofin duniya.










