Argentina v3-0 Uruguay: Lionel Messi ya ci wa Argentina kwallo 80

Lionel Messi (left) is presented with a recognition of his 80 goals by the president of the Argentina football association (right)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lionel Messi ya fara buga wa Argentina wasa a 2005, shekara daya tsakani ya fara ci wa tawagar kwallo

Lionel Messi ya kafa ttarihin zama na farko a Kudancin Amurka da ya zazzaga kwallo 80 a raga.

Ranar Lahadi Argentina ta doke Uruguay 3-0 a wasan neman gurbin buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.

Kyaftin Messi ne ya fara cin kwallo daga baya Rodrigo de Paul ya kara na biyu, sannan Lautaro Martinez ya zura na uku a raga.

"Mun buga kwallo mai kayatarwa. Komai ya tafi yadda ya kamata, in ji Messi.

"Uruguay sun shirya mana kuma sun samu damarmaki masu hatsari. Muna cin kwallon muka fara sararawa, sannan muka kara cin kwallaye.''

Kawo yanzu tawagar Argentina ta yi wasa 24 ba a doke ta ba, kuma wannan nasarar ta kara sa matsi ga Brazil a wasannin Kudancin Amurka a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniy.

Kuma nasarar da Argentina ta yi, wadda take ta biyu a teburi ta rage tazarar maki tsakaninta da Brazil ta daya ya koma shida, bayan Colombia da Brazil suka tashi 0-0 ranar Lahadi.

Karon farko da Brazil ba ta ci wasa ba a fafatawa 10 kenan, bayan da ta yi nasara tara a bana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a badi.