Lionel Messi ya kulla yarjejeniya da Paris Saint-Germain

Bayanan bidiyo, Lionel Messi: Kwallaye goma mafi kayatarwa da ya zura wa Barcelona

Fitaccen dan kwallon kafar duniya, Lionel Messi, ya kulla yarjejeniya da Paris Saint-Germain, kwanaki kadan bayan ya bar Barcelona.

Mai yi wa BBC Sport sharhi kan wasanni Guillem Balague ya tabbatar da hakan.

Dan wasan na Argentina, wanda ya bar Barca ranar Alhamis din da ta gabata, ya kulla yarjejeniyar shekara biyu da kungiyar ta Faransa.

Kwangilar, wadda za a iya tsawaita ta zuwa shekara uku, ba za ta fada ba sai an kammala duba lafiyarsa.

Messi, dan wasan da sau shida yana lashe gasar dan kwallon kafar duniya na Fifa wato Ballon d'Or yana da zabi biyu bayan ya bar Barcelona, amma ya gwammace ya tafi PSG a kan yarjejeniyar da ta kai £25m a shekara bayan an cire haraji.

Matakin da PSG ta dauka na sayen Messi - wanda zai hadu da tsohon abokin wasansa a Barca Neymar - zai zama daya daga cikin hadin 'yan wasan gaba mafi hadari da aka taba yi a tarihin kwallon kafa.

Zai buga wasa a gaba tare da 'yan wasa biyu mafi tsada a duniya - wato Neymar da Kylian Mbappe.

Kungiyar ta PSG wadda Mauricio Pochettino yake jagoranta ta kare kakar bara a gasar Ligue 1 a mataki na biyu bayan Lille wacce ta lashe kofin.

"An tabbatar da wannan yarjejeniya. Lionel Messi zai zama dan wasan PSG," in ji Balague a tattaunawarsa da shirin BBC Radio 5 Live. "Shikenan. Lamarin ya faru ne mintuna kadan da suka wuce.

"A yanzu haka akwai 'yan sanda da yawa kamar 'yan wasa a [a filin kwallo]. Nan gaba kadan komai zai sauya. Akwai kyamarori guda takwas a nan, amma komai zai sauya. Da alama kwangilar shekaa biyu ce, da kuma yiwuwar karin shekara daya.

Dan kwallon na Argentina ya shirye tsawaita zamansa na shekara 21 a Barcelona inda ya amince a zaftare kashi 50 cikin dari na albashinsa.

Sai dai ranar Alhamis ta sanar ranar Alhamis cewa "matsalolin kudi" da dokokin La Liga sun hana ta tsawaita kwangilar dan wasan lamarin da ya tilasta masa yin bankwana da ita.

Dan wasan mai shekara 34 ya ce ya so ci gaba da zama a Barcelona kuma ya yi duk "abin da ya kamata" domin tsawaita zamansa, amma hakan ya gagara.

A picture of Lionel Messi is taken down outside the Nou Camp

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana cire hotunan Lionel Messi daga Nou Camp