Lionel Messi: Abu 10 da kyaftin din Argentina ya yi a Barcelona da ba za a manta da su ba
Da alama dai rayuwar Lionel Messi a Barcelona ta zo karshe.
Kyaftin din na Argentina shi ne dan wasan da ya fi zura wa Barcelona kwallo inda ya ci kwallo 672 sannan ya ci Kofin La Liga guda 10, Kofin Zakarun Turai hudu da kuma Copa del Rey bakwai, da kuma kyautar gwarzon dan kwallon kafar duniya na Fifa wato Ballon d'Or sau shida.
Amma yanzu ba shi da kungiya bayan Barcelona ta ce ba za ta iya sabunta kwangilarsa ba bisa la'akari da dokokin La Liga na tabbatar da adalci wajen kashe kudi kan 'yan wasa.
Ana sa ran kungiyoyi da dama za su ci gaba da neman dan wasan - watakila dai ya tafi Paris St-Germain. Kafin nan, ga 10 daga cikin shahararrun lokuta da ya yi a Barcelona.
Kwallaye uku rigis na farko da Messi ya ci a wasa

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona 3-3 Real Madrid, 10ga watan Maris na 2007
Kwallaye uku rigis a farko da Messi ya ci a wasa guda sun faru ne a daya daga cikin manyan gasar kwallon kafa. Matashin dan wasan ya zura dukkan kwallaye uku da Barca ta ci a wasan hamayya na El-Clasico a shekarar 2007 - kuma shi ne karonsa na farko da ya yi hakan a Nou Camp - ciki har da kwallon karshe da ya zura mai ban sha'awa bayan ya yanka yan bayan Madrid.
Wannan shi ne lokacin da sunansa ya karade duniya.
Kwallon da Messi ya ci wadda ta fi kayatarwa?

Asalin hoton, Rex Features
Barcelona 5-2 Getafe, 18 ga watan Afrilun 2007
Kwallon da Messi ya zura a wasan kusa da na karshe a gasar Copa del Rey shekaru 14 ta kasance wadda ta fi kayatarwa.
A wani salon cin kwallo irin na Diego Maradona (ba wanda ya sa hannu ba) a wasan da Argentina ta yi da Ingila na Gasar cin Kofin Duniya a 1986, Messi ya dauki kwallo, ya 'yan wasa kusan biyar, sannan ya zagaye mai tsaron raga daga nan ya zura kwallon a ragarsu.
Kwallon farko da Messi ya ci a wasan karshe na Gasar Zakarun Turai

Asalin hoton, Rex Features
Barcelona 2-0 Manchester United, 27 ga watan Mayun 2009
Idan za ku yarda, akwai lokacin da mutane suke tambayar cewa ko Messi zai iya kai bantensa a fafatawa da kungiyoyin Ingila a Turai. Ya gaza cin kwallo a wasannin cin Kofin Zakarun Turai 10 da ya fafata da Ingila kafin wasan karshe da aka yi a 2009.
Sai dai an daina tantama bayan da Messi ya yi tsalle a cikin da'ira ya zura kwallon da Xavi ya bugu a wasan na farko na wasan karshe a gasar zakarun Turai - kuma a wasan farko da aka yi wa lakabi da wasa tsakanin Messi da Cristiano Ronaldo.
Shekaru biyu bayan hakan, ya sake zura kwallo a wasan karshe da suka yi da United - shi ne karo na uku cikin wasa hudu da ya ci malbar yabo a gasar Zakarun Turai.
Messi ya zura kwallo hudu a ragar Arsenal

Asalin hoton, Rex Features
Barcelona 4-1 Arsenal, 6 ga watan Afriunl 2010
Messi ya ci kwallaye hudu a karon farko a tarihinsa na kwallon kafa a yayin da ya ragargaji Arsenal a zagayen kwasan kusa da daf da na karshe na gasar Zakarun Turai ta 2010.
Ya kamata mu fadi yadda ya ci kwallaye biyar a wasan da suka yi da Bayer Leverkusen inda suka doke su da ci 7-1 a zagayen 'yan 16 shekaru biyu bayan wasansu da Arsenal.
Shi ne na biyu da ya fi zura kwallo a tarihin gasar Zakarun Turai inda ya ci kwallo 120, bayan Cristiano Ronaldo.
Messi ya kafa tarihin ci wa Barcelona kwallo
Barcelona 5-3 Granada, 20 ga watan Maris na 2012
Messi ya kafa tarihin ci wa Barcelona yana da shekaru 24 - cikin wani sabon salo, inda ya zura kwallo uku a wasa guda.
Ya yi kankankan da taririn da Cesar Rodriguez ya kafa na cin kwallaye 232 a yayin da ya buga wasansa na farko a fafatawa da Granada, inda ya kafa sabon tarihi yayin da ya ci kwallo ta biyu, sannan ya nuna cewa bab kamarsa yayin da ya zura kwallo ta uku.
Messi ya ci kwallaye 91 a shekara daya

Asalin hoton, Getty Images
Real Valladolid 1-3 Barcelona, 22ga watan Disambar 2012
Ko an yi la'akari da kwallaye masu kayatarwa da Messi da Ronaldo suke zurawa, sai an duba yadda dan wasan Argentina ya kafa tariri a 2012 - ya ci kwallaye 91 a shekara daya ta kwallaon kafa.
Ya ci wa Barcelona kwallaye 79 yayin da ya ci wa Argentina kwallaye 12 - a jimullar wasanni 69 da ya yi wa kungiyarsa da kasarsa.
Hakan ya bai wa Messi damar lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar duniya na Fifa sau hudu a jere - ko da yake ya ci Kofin Copa del Rey ne kawai a 2012 kan dukkan kwallayen da ya zura.
Messi ya kafa tarihin cin kwallo a gasar La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona 5-1 Sevilla, 22 ga watan Nuwamba na 2014
Ya sake kafa tarihin cin kwallo - inda ya sake zura kwallo uku a wasa daya.
Messi ya yi kankankan da Telmo Zarra wanda ya ci kwallaye 251 yayin da ya ci kwallo da bugun-tazara, sannan ya kafa nasa tarihin, kana ya kara kwallo ta uku.
Yanzu Messi ya ci kwallaye 474 a gasar La Liga, fiye da kwallaye 200 kenan da wuce wanda ya kafa tsohon tarihi, kuma fiye da 150 a gaban Ronaldo - wanda ya ci wa Real Madrid kwallaye 311 kafin ya tafi Juventus.
Messi ya ci kwallonsa ta 500 a Barcelona lokacin wasan El Clasico

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid 2-3 Barcelona - 23 ga watan Afriunl 2017
Wani lokaci zura kwallo wani abu ne da ba a tsammani - kuma a wannan karon abin da ya faru kenan. Messi ya zura kwallon ne a yayin da aka kara lokaci inda ya ci kwallo a fafatawarsu da Real a 2017, karon farko da ya zura kwallo daga bugun da ya yi daga wajen yadi na 18. Ita ce ta ba su damar yin nasara a wasan hamayya na El Clasico, kuma ita ce kwallo ta 500 da ya ci wa Barcelona abin da ya sa suka zama na daya a saman teburin gasar - ko da yake daga bisani Real ta lashe gasar.
Ya yi murna sosai lokacin da ya tube rigarsa ya rike ta a hannu yadda masu son Bernabeu za su ga sunansa.
Messi ya ci Ballon d'Or karo na shida

Asalin hoton, EPA
Paris, 2 ga watan Disambar 2019
Messi ya ci lambar yabo ta gwarzon dan kwallon kafar duniya na fifa karo na shida a watan Disambar 2019, inda ya sha gaban Ronaldo wanda ya ci lambar yabon sau biyar - bayan ya zi wa kungiyarsa a kasarsa kwallo sau 54 a kakar 2018-19.
Shi ne karon farko da ya samu wannan lambar yabo tun 2012 - sauran ya same su ne a 2015.
"Har yanzu ina da sauran shekaru masu kyawu a gabana," a cewarsa yayin da yake karbar lambar yabon.
Messi ya doke tarihin da Pele ya kafa

Asalin hoton, Getty Images
Real Valladolid 0-3 Barcelona, 22ga watan Disambar 2020
Messi ya ci wa Barcelona karin kwallaye 38 bayan ya bayyana cewa yana son barin kungiyar a bazarar da ta wuce - kuma hakan ya sa ya sake kafa tarihi.
Ya ci kwallonsa ta 644 a Barcelonalokacin wasan da suka buge Real Valladolid gabanin Kirsimeti inda ya doke tarihin da Pele ya kafa - na cin kwallo 643.
Tuni ya dora a kan tarihin da ya kafa inda ya zura kwallaye 672.












