Lionel Messi ya yi wasa na 147 a tawagar kwallon kafar Argentina

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi ya yi wa tawagar kwallon kafa ta Argentina wasa na 147 a karawar da suka doke Paraguay, suka kai daf da na kusa da na karshe a Copa America.
Messi mai shekara 34 ya yi kan-kan-kan da Javier Mascherano wajen yawan buga wa tawagar ta Argentina wasanni.
Argentina ce ta ja ragamar rukuni na daya, bayan da Chile ta tashi 1-1 da Uruguay, wadda itama ta kai zagayen gaba.
Wannan gasar damar ce ta karshe da Messi zai lashe kofi a babbar tawagar Argentina da bai samu damar daukar ba.
Dan wasan Barcelona bai taba lashe kofi a babbar kungiyar Argentina ba, illa dai ya daga kofin duniya a tawagar matasa ta 'yan kasa da shekara 20 a shekarar 2005.
Gasar Copa America da ake yi a Brazil a bana an tsara yi a Argentina tun farko, amma tsoron yada cutar korona ta sa aka dauke gasar daga kasar.
Messi wanda ya lashe Ballon d'Or shida na taka rawar gani a gasar Copa America ta bana, duk da cutar korona da ke kai tsaiko a wasannin.
Saura wasa hudu suka rage a rukunin farko, inda Paraguay keda maki uku, Uruguay daya ne da ita da Bolivia mara maki ko daya.
Hakan na nufin kowacce tana da damar kai wa zagayen gaba, kamar yadda Argentina da Chile suka yi.
Tuni dai Brazil mai masaukin baki ta kai karawar daf da na kusa da na karshe a rukuni na biyu.










