Lionel Messi: Kyaftin din Argentina ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu a PSG

Lionel Messi Contrack signing

Asalin hoton, PSG FC

Kyaftin din Argentina Lionel Messi ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu a Paris St Germain ranar Talata, bayan barin Barcelona.

Kwantiragin mai shekara 34 ta hada da zabin tsawaita ta zuwa kaka daya nan gaba, idan ya taka rawar gani.

Messi ya bar Barcelona kungiyar da ya buga wa tamaula kaka 21, bayan da matsin tattalin arziki ya sa ya hakura da kungiyar, wadda ba za ta iya biyan albashinsa ba.

"Ina fatan bude sabon shafin tamaula a sana'ata ta kwallon kafa a Paris. Kungiyar da tunaninta da hangen nesanta ya yi iri daya da wanda nake da shi," in ji dan kwallon Argentina.

"Na kwan da sanin kwazon 'yan wasan kungiyar da jami'anta. Na zo nan ne don na dora kan ginin da aka yi tare da 'yan wasa, wani abu mahimmi ga PSG da magoya baya. Zan so naga na saka kafata a katafaren filin Parc des Princes."

Shugaban PSG, Nasser al-Khelaifi ya ce: "Na kasance mai farinciki da Lionel Messi ya zabi buga wa Paris St-Germain tamaula, muna alfahari muna masa maraba da zuwa birnin Paris da iyalansa.

"Kara samun Leo da muka yi a kungiyarmu ya tabbatar da kara samun nasarar dauko fitattun 'yan kwallon duniya. Tare da kwararren kocinmu da ma'aikatansa. Ina fatan ganin kungiyarmu ta kafa samun nasarori da magoya bayanmu za su yi alfahari a duniya.''

Wanda ake cewa daya ne daga fitattun 'yan kwallon duniya a wannan karnin. Messi ya ci kwallo 672 a wasa 778 da ya yi wa Barcelona, wadda ya koma tun yana da shekara 13.

Dan wasan ya lashe kyautar Ballon d'Or karo shida, ya kuma dauki kofi 35 a kungiyar ta Sifaniya.

Shine na hudu da PSG da dauka a bana, bayan dan kwallon Netherlands, Georginio Wijnaldu da mai tsaron bayan tawagar Sifaniya, Sergio Ramos da golan Italiya, Gianluigi Donnarumma.

Haka kuma ta dauki fitattcen dan kwallon tawagar Morocco, Achraf Hakimi mai tsaron baya daga Inter Milan.

Messi, wanda aka bai wa riga mai lamba 30 zai buga gurbin gaba tare da 'yan wasa mafi tsada a duniya - Neymar da kuma Kylian Mbappe.

Watakila Messi ya fara buga wa PSG tamaula a wasan da za ta kara a gida da Strasbourg ranar Asabar.