Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Lukaku, Aguero, Romero, Odegaard, De Ligt, Milenkovic, Ward-Prowse
Paris Saint-Germain za ta bai wa Lionel Messi kwangilar shekara biyu a taron da za a yi tsakanin manyan jami'an kungiyar da mahaifin Messi ranar Asabar. (Telegraph - subscription required)
Mahaifin Messi ya tuntubiParis St-Germain domin sanin ko a shirye kungiyar ta Faransa take ta dauki dan wasan mai shekara 34. (Marca)
Mai kungiyar kwallon kafarChelsea Roman Abramovich ya nemi gudanar da "taron gaggawa" da wakilan Messi bayan an sanar cewa dan wasan na Argentina ba zai ci gaba da zama a Barcelonaba. (AS, in Spanish)
Kocin PSG Mauricio Pochettino ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar su dauki Messi kuma idan dan wasan na Argentina ya tafi kungiyar ta Ligue 1 hakan zai iya sanya wa dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya sabunta kwangilarsa sannan matakin zai iya sa wa kungiyar ta kawo karshen neman da take yi wa Paul Pogba, mai shekara 28, daga Manchester United. (ESPN)
Shi kansa Messi yana son tafiya Manchester City domin sake haduwa da kocinta Pep Guardiola a matsayin zabinsa na farko. (Mail)
Dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 29, ya nemi bai wa Messi rigarsa mai lamba 10 a Paris Saint-Germain a wani yunkuri na rarrashinsa ya tafi kungiyar da ke buga gasar Ligue 1. (RMC Sport via Get French Football News)
An ce dan wasan Argentina Sergio Aguero, mai shekara 33, wanda ya tafi Barcelona a watan Mayu bayan ya bar Man City, yana son barin Catalan bayan an sanar cewa babban abokinsa Messi ba zai ci gaba da zama a Nou Camp ba. (Beteve - in Catalan)
Chelsea na samun karin karfin gwiwa domin kulla yarjejeniya da Inter Milan a karshen mako saboda sake daukar Romelu Lukaku, inda kocin kungiyar Thomas Tuchel yake son ya kammala daukar dan wasan kafin a soma kakar wasa. (Standard)
Chelsea ta gwammace ta bayar da kudi tare da wani dan wasan domin a ba ta dan wasan Belgium mai shekara 28, yayin da Inter take son a biya ta kudi zalla. (Sky Sports)
Lukaku ya amince da sharudan da Chelsea ta gindaya masa kuma yana jiran kungiyoyin biyu su kammala kulla yarjejeniya a kansa. (football.london)
Barcelona ta amince da sharudan da dan wasan Portugal Renato Sanches, mai shekara 23, ya mika mata ko da yake ba ta kai ga amincewa da kudin daLilletake son ta karba kan dan wasan ba. (Le10 Sport)
West Ham tana ci gaba da ttaunawa da Fiorentina a kan yarjejeniyar sama da £14m domin daukar dan wasan Serbia Nikola Milenkovic, mai shekara 23, amma za ta iya fuskantar kalubale daga Juventus. (Mail)
Real Madrid ta hana dan wasan Norway mai shekara 22 Martin Odegaard tafiya Arsenal bayan Toni Kroos ya ji rauni. (AS, via Team Talk)