Lionel Messi: Barcelona ta ce dan kwallon Argentina ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba

Barcelona ta ce Lionel Messi ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba, sakamakon matsin tattalin arziki.

Messi, mai shekara 34, bai da yarjejeniya da wata kungiya, tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Camp Nou a karshen watan Yuni.

Ya amince da sabuwar kunshin kwantiragi da rage albashinsa a kungiyar, sai dai Barcelona ta dogara da idan ta sayar da wasu 'yan wasan ta biya albashinsa.

Barcelona ta ce Messi ya yi niyar tsawaita kwantiraginsa a Camp Nou da nufin saka hannu ranar Alhamis, amma ta soki hukumar La Liga kan dokar daidaita kashe kudin kungiya da hakan ya yi mata cikas.

Ƙungiyar ta ce, "Duk da cewa Barcelona da Lionel Messi sun cimma yarjejeniya da kuma amincewa kan ƙulla sabuwar yarjejeniya a yau, hakan ba zai yiwu ba saboda matsalolin kuɗi da wasu tsare-tsaren ƙungiyar.

"FC Barcelona tana matuƙar godiya ga ɗan wasan sakamakon rawar ganin da ya taka wa ƙungiyar kan gudunmowarsa ga ci gabanta tana kuma yi masa fatan alkheri a rayuwarsa ta ƙwallo ta gaba da kuma ta ƙashin kansa," a cewar ƙungiyar.