Wadanda Bayern Munich ta dauka da wadanda suka bar kungiyar

Bayern Munich na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar kakar tamaula ta 2021-22 don ganin ta taka rawar gani a bana.

Cikin shirye-shiryen da take yi ta buga wasan sada zumunta da Koln da ta yi rashin nasara da ci 3-2 ranar 17 ga watan Yuli.

Ta kuma yi 2-2 da Ajax a Audi Cup ranar 24 ga watan Yuli, sannan ranar 28 ga watan Yuli ta doke Borussia Monchengladbach da ci 2-0.

Bayern Munich ta sha kaci da ci 3-0 a hannun Napoli a gasar Audi Cup ranar 31 ga watan Yuli.

Ranar 13 ga watan Agusta, Bayern Munich za ta fara buga Bundesliga na bana da Borussia Mönchengladbach.

Daga nan kuma Bayern ta kara da Borussia Dortmund a German Super Cup ranar 17 ga watan Agusta.

Wadanda Bayern Munich ta dauka a bana:

Dayot Upamecano daga RB Leipzig

Omar Richards daga Reading

Sven Ulreich daga Hamburg

Wadanda suka koma koma Bayern, bayan zuwa wasannin aro:

Michael Cuisance daga Marseille

Adrian Fein daga PSV Eindhoven

Christian Früchtl daga Nuremberg

Lasse Günther daga Augsburg

Chris Richards daga Hoffenheim

Joshua Zirkzee daga Parma

Wadanda suka bar kungiyar:

David Alaba zuwa Real Madrid

Angelo Stiller zuwa Hoffenheim

Jerome Boateng kwantiragi ce ta kare a kungiyar

Javi Martinez kwantiragi ce ta kare a kungiyar

Wadanda ta bayar da su aro don buga kakar bana:

Fiete Arp zuwa Holstein Kiel

Adrian Fein zuwa Greuther Fürth

Lars Lukas Mai zuwa Werder Bremen

Alexander Nübel zuwa Monaco

Sarpreet Singh zuwa Jahn Regensburg

Joshua Zirkzee zuwa RSC Anderlecht

Wadanda suka kammala buga mata wasannin aro:

Douglas Costa daga Juventus

Tiago Dantas daga Benfica