Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Kane, Lukaku, Correa, Trippier, Aouar, Abraham, Armstrong
Sanawar da Barcelona ta bayar cewa dan wasan gaban Argentina Lionel Messi, mai shekara 34, ba zai ci gaba da zama a kungiyar ba ta "bude kofa ta daukar matakin ba-zata na tafiyarsa" Manchester City. (Manchester Evening News)
Kazalika kasancewar Messi a matsayin maras kungiya za ta yi tasiri kan yunkurin da Man City take yi na sayen dan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27. (Express)
Ana alakanta Paris St-Germain da yin gaggawa wajen neman daukarMessi, kuma ana sa ran dan wasan na Argentina zai iya tafiya kungiyar. (Le Parisien - in French)
Duk da yake ana ganin dan wasan na Argentina wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau shida zai iya tafiya PSG, amma ba a fitar da rai kan cewa zai iya tafiya Amurka ba domin buga tamaula a Major League Soccer. (Mail)
Mai yiwuwa a fuskanci jinkiri na komawar Romelu Lukaku Chelsea a yayin da shugaban Inter Milan Steven Zhang yake son ya yi nazari kafin ya yanke shawara kan ko zai sayar da dan wasan na Belgium mai shekara 28. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester United tana ci gaba da zawarcin Kieran Trippier, amma Atletico Madrid ta ki sallama dan wasan na Ingila mai shekara 30 a kan £34m. (Sun)
Arsenal ta taya dan wasan Argentina da ke murza leda a Lazio Joaquin Correa, mai shekara 26, a kan £17m abin da kungiyar da ke Rome take "gani a matsayin farashin da bai dace ba" . (Corriere dello Sport, via Sport Witness)
Southampton ta nemi karbar aron Tammy Abraham, mai shekara 23, dagaChelsea a yayin da ta soma neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila Danny Ings, mai shekara 29, wanda ya tafi Aston Villa a farkon makon nan. (Talksport)
Arsenal na shirin daukar golan Ingila Aaron Ramsdale da dan wasan tsakiyar Norway Sander Berge daga Sheffield United, amma mai yiwuwa kudin da ta take son mikawa £50m domin daukar 'yan wasan masu shekara 23 ba zai isa ba. (Star)
Dan wasan tsakiyarLyon dan kasar Faransa Houssem Aouar, mai shekara 23, yana bijirewa kan tafiya Arsenal a bazarar da muke ciki. (Sun)
Leicester ta kara kaimi wajen neman dan wasan baya bayan dan wasan Faransa da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Wesley Fofana, mai shekara 20, ya karye lokacin wasan sada zumunci da suka yi ranar Laraba da Villarreal. (Sky Sports)