Manchester City ta kusan sayen Grealish kan fam miliyan 100 daga Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta kusan daukar Jack Grealish daga Aston Villa kan fam miliyan 100.
Za a kammala cinikin da wuri domin dan kwallon tawagar Ingila ya samu damar bugawa Manchester City Community Shield da za ta kara da Leicester City ranar Asabar.
Idan cinikin ya fada, Grealish mai shekara 25, zai zama dan kwallo mafi tsada da aka saya a Burtaniya.
Cinikin dan wasan Aston Villa zai haura wanda Manchester United ta sake daukar dan wasan tawagar Faransa, Paul Pogba daga Juventus a 2016 kan fam miliyan 89.
Tun farko Grealish ya yi shirin komawa Aston Villa da fara atisaye domin tunkarar kakar da za mu shiga, bayan hutun gasar Euro 2020 da ya wakilci Ingila.

Grealish ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a Aston Villa a cikin watan Satumba.
Guardiola na fatan kwarewar da Grealish keda ita a wasan tamaula zai kara bunkasa kwazon kungiyar.
City ta zura kwallo 83 a gasar Premier League da ta karkare da tazarar kwallo 10 tsakaninta da Manchester auanited, amma Guardiola na ganin ya kamata su kara kwazo a fannin zazzaga kwallaye a raga.
Kwazon Grealish da 'yan gaban Man City:
Ranar Litinin Villa ta sanar da daukar Leon Bailey kan fam miliyan 25 da daukar Emiliano Buendia daga Norwich City da kuma Ashley Young daga Inter Milan.
Idan City ta dauki Grealish kan fam miliyan 100 zai zama na tara da aka saya mafi tsada a tarihi.
'Yan wasa takwas ne aka saya fam miyan 100 ko fiye da haka kawo yanzu:
Wadanda aka saya mafi tsada a duniya:
Neymar [Barcelona - Paris St-Germain] £200m a 2017
Kylian Mbappe [Monaco - Paris St-Germain] £166m a 2017
Philippe Coutinho [Liverpool - Barcelona] £142m a 2018
Ousmane Dembele [Borussia Dortmund - Barcelona] jumullar kudin £135m a 2017
Joao Felix [Benfica - Atletico Madrid] £113m a 2019











