Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Kane, Grealish, Ronaldo, Bale, White, Trippier, Zaha, Locatelli

Kane ya ci kyautar wanda ya fi zura kwallo ta Golden Boot a Premier da ta gwanin dan wasa a kakar 2020-21 , da ta yawan zura kwallo a gasar kofin duniya na 2018 a Rasha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kane ya ci kyautar wanda ya fi zura kwallo ta Golden Boot a Premier da ta gwanin dan wasa a kakar 2020-21 , da ta yawan zura kwallo a gasar kofin duniya na 2018 a Rasha

Har yanzu dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, mai shekara 27, da na Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 25, su ne wadanda Manchester City ta fi son gani ta saya a bazaran nan.

Kuma zakarun na Premier sun kuduri aniyar lalle sai sun sayi dukkanin 'yan wasan biyu na tawagar Ingila. (Jaridar Athletic)

Sai dai kuma ana sa ran tauraron dan wasan na Villa, Grealish, ya kulla sabuwar yarjejeniya da kungiyar tasa. (Birmingham Mail)

Bisa ga dukkan alamu dole Real Madrid ta hakura ta ci gaba da zama da dan gabanta, Gareth Bale tsawon wata kakar daya saboda babu wata kungiya da ta taya dan wasan na Wales mai shekara 32, wanda ya yi zaman aro a tsohuwar kungiyarsa Tottenham a kakar da ta gabata. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Gareth Bale na karbar albashin kusan fam dubu 600 a sati a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gareth Bale na karbar albashin kusan fam dubu 600 a sati a Real Madrid

Arsenal ta cimma yarjejeniyar baka da Brighton a kan cinikin dan bayan Ingila Ben White, mai shekara 23, a kan kusan fam miliyan 50. (Athletic)

Crystal Palace na fatan kokarin da sabon kociyanta Patrick Vieira yake yi na karfafa kungiyar zai isa shawo kan dan wasan gabanta na Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 28, ya hakura ya ci gaba da zama a kungiyar. (Standard)

Inter Milan ta kara ci gaba da kokarin ganin ta dauko dan wasan baya, dan Sifaniya Hector Bellerin daga Arsenal, amma kuma zakarun na Italiya, na son karbar dan wasan mai shekara 26 ne a matsayin aro na shekara daya, da zabin sayensa dindindin a badi, yayin da ita Arsenal ke son kusan fam miliyan 15 a kansa. (Sun)

Dan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, da ake cewa zai koma tsohuwar kungiyarsa Manchester United ko Paris St-Germain, ga alama zai ci gaba da zama a Juventus tsawon karin shekara daya, amma za a rage masa yawan albashi. (Gazzetta dello Sport)

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Mai yiwuwa sabon kociyan Tottenham Nuno Espirito Santo ya nufi tsohuwar kungiyarsa Wolves domin neman sabbin 'yan wasa a bazaran nan, inda ake ganin zai bukaci sayen dan bayan Ivory Coast Willy Boly, mai shekara 30, da dan gaban Portugal Daniel Podence mai shekara 25. (talkSport)

Nuno Espirito Santo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nuno Espirito Santo

Har yanzu Arsenal na sha'awar dan wasan tsakiya na Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, bayan zaman aro da ya yi a kakar da ta wuce, kuma kociyan Mikel Arteta a shirye yake ya neme shi idan Real Madrid za ta bar shi ya sake zuwa Gunners din. (Athletic)

Burnley ta doke zakarun Turai Chelsea a gasar sayen mai tsaron ragar Wales Wayne Hennessey mai shekara 34, bayan da ya bar Crystal Palace . (Football Insider)

Harry Wilson na daga cikin 'yan wasa 10 da Liverpool ke son sayarwa, kuma za ta karbi fam miliyan 10 a kan dan gaban na Wales mai shekara 24, wanda ake cewa zai tafi Brentford, ko West Brom ko kuma Benfica. (Mirror)

Sassuolo na shirin sayen dan wasan tsakiya na Liverpool, dan Serbia Marko Grujic, mai shekara 25, idan har Manuel Locatelli, na tawagar Italiya, mai shekara 23, da ake cewa zai koma Arsenal ko Juventus, ya bar kungiyar a bazaran nan. (Sky Sports)

Liverpool da Manchester United ma na sha'awar dan wasan tsakiya na Atletico Madrid, na Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26 da ake alakantawa da tafiya Barcelona a matsayin musaya da Antoine Griezmann, mai shekara 30. (AS)

Sai dai Atletico ce kan gaba wajen damar daukar tsohon dan wasan nata Griezmann, amma kuma an sanar da Chelsea, da Manchester City da kuma Liverpool cewa an rage farashin dan gaban na Faransa.

Akalla kungiyoyin Premier biyu ne da ba a furta sunayensu ba suka yi magana da wakilinsa a watan da ya gabata. (90min)

Liverpool ka iya motsawa domin neman sayen dan wasan tsakiya na Lyon, dan Faransa Houssem Aouar, mai shekara 23,wanda rahotanni ke cewa zai koma Tottenham ko Arsenal ko kuma Manchester United. (ESPN)

Houssem Aouar (a hagu) da Raheem Sterling na Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Dan bayan Ingila Kieran Trippier, mai shekara 30 na da kwarin guiwar tafiya Manchester United daga Atletico Madrid a bazaran nan, kuma daman ya shirya tafiya tun kafin fara gasar Turai ta Euro 2020an. (Manchester Evening News)

Valencia na daga cikin kungiyoyin Sifaniya da ke sha'awar dan gaban Leeds United Helder Costa mai shekara 27. (Athletic)

An yi watsi da bukatar Aston Villa ta neman sayen dan gaban Northampton Town Caleb Chukwuemeka mai shekara 19. (Mail)

Kungiyar Jose Mourinho Roma, da Rennes ta Faransa da kuma Arsenal, sun nuna sha'awarsu ta sayen dan wasan tsakiya na kungiyar AZ Alkmaar, dan Holland Teun Koopmeiners mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin Granit Xhaka, mai shekara 28 da ake ganin zai tafi Roma. (De Telegraaf)

Dan bayan North Macedonia Ezgjan Alioski, mai shekara 29, na shirin tafiya Galatasaray a matsayin wand aba shi da kungiya, a kwantiragin shekara uku, bayan da ya yi watsi da tayi har biyu na sabunta zamansa a Leeds United. (Football Insider)