IMN ta nemi a sako Sheikh Zakzaky ba tare da sharadi ba

Asalin hoton, OTHERS
Kungiyar 'yan Shi'a ta haraka Islamiyya a Najeriya IMN, ta yi kira ga gwamnatin kasar ta saki jagoranta Sheikh Ibrahim Elzakzaky, da ya kwashe shekara hudu a hannun hukuma.
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS na tsare da jagoran Shi'an da matarsa Zeenat da wasu 'yan kungiyar bayan wani rikici tsakanin mabiyan malamin da jam'ian tsaro.
Hukumomi na zargin mutanen da aikaita manyan laifuka da suka tunzura jama'a da gudanar da haramtaccen taro da yin sanadiyyar mutuwar mutane.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa ya fitar, kungiyar ta ce:
"Yayin da muke tunawa da zagayowar ranar kisan kiyashin Zariya da mutuwar mambobin IMN, muna kira da a gaggauta sakin Sheikh tare da duk sauran jama'ar da ke tsare ba tare da wani sharadi ba."
IMN na kuma bukatar a hukunta dukknain sojojin da take zargi da hannu a "kisan 'yan kugiyar kusan mutum kusan 1000" a Zariya.
A makon jiya ne wata kotu ta bayar da umarnin a mayar da shi gidan yari "domin samun ganawa da likitocinsa da lauyoyinsa cikin sauki".
Hakan ya zo ne bayan babban lauyan da ke kare Zakzaky Femi Falana ya sanar da kotun cewa ba sa iya ganin wadanda suke karewar a hannun DSS.
Hakan ya haifar da cecekuce, inda magoya bayan malamin suka yi tir da umarnin na kotu, yayin da wasu masana fannin shari'a ke ganin kotun ta yi abin da tuni ya kamata ta yi.
Amma kuma wasu na ganin hakan zai taimaka wa malamin yayin da za a ci gaba yi masa shari'a.
Me hakan ke nufi ta fuskar shari'a?
BBC ta yi hira da Barista Sunusi Musa kuma ya ce kotu tana da damar ta fadi inda ya dace a ajiye wanda ake tuhuma da laifi.
''Na farko a doka abin da ya dace a yi shi ne duk lokacin da jami'an tsaro ko 'yan sanda ko wata hukuma da aka ba ta damar gurfanar da wani a gaban kotu to ta kai shi gaban kotun," Barista Sunusi ya fada.
Ya ci gaba da cewa: "Daga ranar yake fita daga hannunsu, ya koma hannun kotu, inda daga nan ne kotun za ta kai shi gidan yari.'
"Wani lokacin kotu ta kan duba wasu dalilai, ko wanda ake tsarewar kan bukaci maimakon a kai shi gidan yari gara an bar shi a hannun hukuma kamar misali hukumar EFCC ko DSS.
"Watakila yana ganin rikon da ake yi masa a wadannan wuraren an fi kula da shi, ko mutuntawa ba kamar gidan yari ba.
"A nan kotun idan ta ga dama kuma tana ganin shi ne adalci ko ya fi maslaha, to za ta iya amincewa da zamansa a wurin hukumomin, ba lallai sai an kai shi gidan kaso ba.''











