Kotu ta ba da umarnin kai el-Zakzaky da matarsa gidan yari

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu da ke zama a Kaduna ta yanke hukuncin mayar da jagoran kungiyar IMN a Najeriya Sheikh Ibraheem el-Zakzaky da matarsa gidan yari daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis da safe, inda ta ce za a mayar da su gidan yarin ne don lauyoyinsu da likitocinsu su samu damar ganinsu cikin sauki.
Tun watan Disambar shekarar 2015 gwamnatin Najeriya ke tsare da malamin biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin mabiyansa da jam'ian tsaro a Zariya.
Sai dai el-Zakzaky da matarsa Zeenatu ba su je kotun ba a ranar Alhamis, kuma lauyansu ya ce rashin zuwan nasu na da alaka da halin rashin lafiya da suke ciki ne.
A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Najeriya ta bayar da izinin fita da Sheikh Zakzaky Indiya don neman magani, sai dai kwanansa uku kacal ya koma kasarsa yana mai zargin cewa ba a bar shi ya ga likitocinsa ba.
Alkalin Mai Shari'a Gideon Kudafa ya daga ci gaba da sauraron shari'ar har zuwa 9 ga watan Fabrairun 2020.
A watan Maris ne Mai Shari'a Gideon Kudafa ya daga sauraren karar har sai baba ta gani sakamakon sanya shi cikin mambobin kotun sauraron kararrakin zabe.
Yadda Shi'a take a Najeriya

Asalin hoton, AFP
- 'Yan Shi'a tsiraru ne a Najeriya, amma rahotanni na nuna cewa yawansu na karuwa
- Kungiyar IMN, wadda aka kafa a shekarun 1980, ita ce babbar kungiyar 'yan Shi'a wadda Ibraheem Zakzaky ke jagoranta
- Tana gudanar da makarantu da asibitocinta a wasu jihohin arewacin kasar
- Kungiyar tana da tarihin arangama da jami'an tsaro
- IMN tana samun goyon bayan Iran inda 'yan Shi'a suke da rinjaye, kuma 'yan kungiyar na yawan zuwa Iran karatu
- Kungiyar Boko Haram da ke ikirarin bin mazhabin Sunna tana kallon 'yan Shi'a a matsayin fandararru, kuma ta sha kai musu hari
Ga rahoton da Nura Mohammed Ringim ya turo mana daga Kaduna :













