An samu baraka tsakanin mabiya Zakzaky

Zakzaky

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Tun shekarar 2015 gwamnatin Najeriya take tsare da malamin addinin
Lokacin karatu: Minti 1

Wata da ke ikirarin cewa 'ya ce ga jagoran mabiya kungiyar `yan uwa Musulmi wadda gwamnatin kasar ta ayyana ta a sahun kungiyoyin ta`addanci mai suna Suhaila Ibrahim Elzakzaky ta bukaci mutanensu da su ci gaba da zanga-zargar da suke yi ta neman a sake jagoran nasu.

Wannan matsayin nata ya ci karo da na mai magana da yawun kungiyar, wanda ya ce sun dakatar da zanga-zangar da suke yi, kasancewar sun shigar da kara a kotu suna kalubalantar matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na haramta wanzuwar kungiyar.

Wasu dai na ganin cewa wannan karon da suke yi da juna a kan matsayinsu, wata alama ce da ke nuna cewa an samu baraka a tsakanin magoya bayan `yan kungiyar.

Matashiyar ta nanata kira ne ga magoya bayansu da su ci gaba da zanga-zanga kamar yadda suka saba a kowace rana.

Ta kara da cewa kungiyarsu ba ta da wani tsayayye a matsayin kakakinta. "Ibrahim Musa shugaba ne kawai na wani gangami da suke da shi da ya shafi harkokin watsa labarai," in ji ta.

Kuma ta ce kungiyar tana da irin wannan gangamin daban-daban da suka shafi wasu harkokinsu.

Ta ce sanarwar da ya bayar "za ta dama wa kungiyarsu lissafi ne kawai," musamman maganar da ya yi cewa sun dakatar da zanga-zanga kuma "duk wanda aka gani yana zanga-zanga to ko jami'in tsaro ne, ko kuma wani wanda yake so ya bata masu suna ne."

Suhaila ta ce ba haka ba ne domin za su "ci gaba da zanga-zangar har sai an saki Sheikh Zakzaky."