Ibrahim Zakzaky ya koma Najeriya

Ibrahim Zakzaky

Asalin hoton, SODIQ ADELAKUN

Bayanan hoto, An dade ana takaddama tun bayan kame Zakzaky da wasu magoya bayansa

Jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ya koma gida daga Indiya kwana uku kacal bayan ya je neman magani, yana mai zargin cewa ba a bar shi ya ga likitocinsa ba.

Wani fasinja a jirgin Ethiopian Airlines ya shaida wa BBC cewa tare suka taho da malamin har suka sauka a filin jirgin sama na Abuja.

Shi ma Abdullahi Usman na kungiyar IMN ya shaida wakilin BBC Chris Ewokor cewa shugaban nasu ya iso Abuja daga birnin Delhi ta Addis Ababa da misalin 12 na rana, amma jami'an tsaro sun fice da shi ba tare da barin 'yan jarida sun ganshi ba.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta ce "mummunar halayyar da ya rinka nunawa tare kokarin neman mafaka ne" ya sa aka mayar da shi gida.

Wakilin BBC Ibrahim Isa, wanda ya halarci filin jirgin saman, shi ma bai samu ganin malamin ba.

Takaddama

Tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin "bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa", sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan "mummunar halayyar da ya nuna".

Ta kara da cewa ya saba ka'idojin kasa da kasa tare da yunkurin neman mafaka, lamarin da ya sa aka mayar da shi gida.

Tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin "bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa", sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan "mummunar halayyar da ya nuna".

Ibrahim Zakzaky

Asalin hoton, Twitter/@SZakzakyOffice

Bayanan hoto, An dade ana takaddama tsakanin lauyoyin gwamnati da na Zakzaky kan tafiyarsa Indiya

A farkon watan nan ne wata kotu a Kaduna ta bai wa malamin da mai dakinsa Zeenat, izinin tafiya Indiya domin duba lafiyarsu bayan shafe shekara kusan hudu a hannun jami'an tsaron Najeriya bisa zargin tayar da zaune-tsaye da yunkurin kisa.

Tun bayan kama shi a watan Disambar 2015, ake samun taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayansa a kasar, inda aka yi hasarar rayuka da kuma dukiyoyi da dama.

Me zai faru da shi bayan ya sauka?

Ganin yadda aka samu kiki-kaka a Indiyar, da kuma yanke shawararsa ta komawa Najeriya, za a iya cewa zai koma hannun gwamnati ne kai tsaye kamar yadda yake kafin ya tafi Indiya.

Saboda izinin da aka ba shi na tafiya asibiti ne kawai, ba wai beli ba ne.

Ibrahim Musa ya ce malamin zai sake neman komawa wata kasar ne tun da dai kotu ta riga ta ba shi damar zuwa a duba lafiyarsa.

"Babu wani rudani domin kotu ta riga ta ba shi dama. Kuma Malam ya ce kasashen Turkiyya da Malesiya da Indunisiya dukka sun ce za su iya yi masa wannan aiki," a cewar Ibrahim Musa.

Sai dai wasu na ganin batun sake fitarsa ba lallai ne ya zo da sauki kamar yadda magoya bayansa ke hasashe ba, ganin irin takaddamar da batun zuwansa Indiya ya haifar tun farko.

Ana hasashen cewa idan har zai sake komawa kasar waje, to sai kotu ta sake bayar da wani sabon umarni, domin wannan umarnin na tafiya Indiya ne kawai kuma ya je ya dawo.