Anelka ya bai wa Mbappe shawarar ya bar PSG

Asalin hoton, Getty Images
Nicolas Anelka ya bai wa Kylian Mbappe shawara cewar idan yana son zama fitatcen dan kwallon kafa a duniya kamar Cristiano Ronaldo ko kuma Messi sai ya bara Paris St Germain.
Mbappe, wanda ya ci kwallo 42 a dukkan wasannin da ya buga wa PSG a kakar da aka kammala, yana da yarjejeniyar da za ta kare da kungiyar a 2022.
Sai dai kuma ana ta alakanta dan wasan tawagar Faransa da cewar zai koma Sifaniya da taka leda a Real Madrid.
Mai shekara 22 ya ci karo da cikas a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020, wanda ya kasa cin fenariti da ta kai Switzerland ta fitar da Faransa a wasan zagaye na biyu da ci 5-4, bayan tashi 3-3.
''Idan yana son lashe kyaututtuka, ya kamata ya bar PSG,'' kamar yadda Anelka ya rubuta a shafinsa na jaridar The Athletic.
''Ba za kace kana gogayya da fitattun 'yan wasa idan kana taka leda a PSG, idan kana son lashe Ballon d'Or, kamar yadda Ronaldo da Messi suka taka rawar gani, dole sai ya yi gumurzu da sanannun 'yan kwallo a duniya.''
Anelka wanda ya lashe gasar Turai a 2000 da tawagar Faransa ya ce gasar Ligue 1 ba sauki, amma Premier League ita ce mai wahalar bugawa''.
''Da zarar kana bukatar yin fice a fanni tamaula a duniya fiye da rawar da ya taka a PSG, ya kamata ya koma Chelsea ko Manchester United ko Arsenal ko Manchester City ko kuma Liverpool. Ko kuma ya koma Sifaniya tare da Real Madrid ko Barcelona. Ko kuma watakila Italiya,'' kamar yadda Anelka ya fada. ''Daga nan za mu fara ganin tasirinsa a tamaula a duniya.''











