Southampton ta tisa keyar Arsenal mai rike da kofin FA gida

Southampton ta yi waje rod da Arsenal a gasar FA a ranar Asabar, bayan kwallo daya mai ban haushi da Arsenal ta ci kanta a minti na 24.

Dan wasan Arsenal na baya Gabriel ne ya ci gida bayan Kyle Walker-Peter ya kwaso wata kwallo a zagayen farko na wasan.

Wannan ce kwallon farko da aka ci Arsenal cikin minti 508 da suka buga, rashin nasara ta farko da suka yi a wasa bakwai da suka buga.

Yanzu dai Southampton za ta kara da kungiyar Wolves mai buga gasar Premier a wasanta na gaba

Arsenal ta fito ne ba tare da dan wasan ta na gaba ba, Pierre-Emerick Aubameyang da kuma na tsakiya Emile Smith Rowe, sai kuma wani dan wasan nata mai tasiri da ta ajiye a canji Bukayo Saka wanda ya shiga daga baya.

Bangaren Mikel Arteta ba su kai wasu hare-hare ba a minti 45 na farkon wasan, sai dai kuma a zagayen na biyu suka tayar da ƙayar baya amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.