Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Rice, Van Dijk, Pogba, Bertrand, Ings, Moyes, Odegaard

Dan wasaan West Ham Declan Rice mai shekara 22 na iya barin kungiyar zuwa karshen kakar wasan nan kan fam miliyan 50, kuma ana jin Chelsea, Liverpool, Manchester City da Manchester United za su fafata kan ganin wanda zai mallake shi. (90 Min)

Liverpool za ta fara daidaita wa da Virgil Van Dijk, dan wasan baya na kasar Holland mai shekara 29 gabanin tattaunawa kan tsawaita zaman Mohamed Salah mai shekara 28. (Eurosport)

Manchester United da dan wasan tsakiya Paul Pogba za su jinkirta yanke hukunci kan zaman dan wasan mai shekara 27 a kungiyar har sai karshen wannan kakar wasan, ko Man Utd na iya lashe gasar a bana. (Mail)

Arsenal na tunanin dauko Ryan Betrand, dan wasan baya kuma da kungiyar Southampton da Ingila wanda shekarunsa 31 domin ta samar wa Kieran Tierney abokin gwagwarmaya. (Evening Standard)

Haka kuma Gunners na da karfin gwuiwar dauko aron Martin Odegaard, mai shekara 22, daga Real Madrid. (Goal)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya nisanta kansa daga rade-dadin da ake yi cewa suna son dauko Danny Ings, dan wasan gaba mai shekara 28 daga Southampton. (Express)

Brendan Rodgers wanda shi ne kocin Leicester City na iya dauko wanda zai gaji Jamie Vardy domin akwai Osdonne Edouard, dan wasan gaba na Celtic mai shekara 23. (Talksport)

West Ham na shirin tsawaita zaman kocinta David Moyes a kungiyar a karshen wannan kakar wasan ta bana. (Guardian)

Kocin Real Sociedad Imanol Alguacil an kusa kammala tattauanawa kan Willian Jose dan wasan gaba na Brazil mai shekara 29 daga Wolves . (Goal)

Liverpool da Manchester United na sa ido kan Jamal Musiala, dan wasan Bayern Munich mai shekara 17 domin da alama ba za a tsawaita zamansa a Bayern din ba.. (Express)