Zinadine Zidane: Kocin Real Madrid ya kamu da Covid-19

Kungiyar Real Madrid ta Sifaniya ta ce kocinta mai shekara 48 Zinadine Zidane ya kamu da cutar korna.

Sai dai kungiyar ba ta yi karin bayani ba kan halin da yake ciki, ko kuma wani dan wasa a cikin tawagar ya kamu.

Zidane na cikin tsaka mai wuya saboda rashin kokarin kungiyar, ciki har da kashin da kungiyar ta sha a ranar Laraba a gasar Copa del Rey a hannu Alcoyano 'yan mataki na uku.

Real ce ke matsayi na biyu inda take biye wa abokiyar hamayyarta da suke birni daya Atletico, kuma za ta kara da Alaves ne a wasan gaba a ranar Asabar.

.Ba kora su gida daga wannan gasar ba ne abin takaici, rashin nasarar ta zo ne bayan waje rod da Athletic Bilbao ta yi da kungiyar makon da ya gabata a gasar Super Cup - Kungiyar na yunkurin buga wasa na takwas ba tare da an doke ta ba a gasar La Liga idan ta yi nasara a kan Alaves.

Real da ke matsayi na biyu a teburin gasar bayan wasa 18 da aka buga, na da tazarar maki bakwai tsakaninta da Atletico wadda ke da wasa daya kwantai a hannunta.