Kevin de Bruyne: Dan kwallon Manchester City zai yi jinyar makonni hudu zuwa shida

Dan kwallon Manchester City, Kevin de Bruyne zai yi jinyar makonni hudu zuwa shida saboda rauni a bayan cinyarsa, in ji Pep Guardiola.

Dan wasan Belgium mai shekaru 29 ya ji rauni ne a ranar Laraba lokacin wasansu da Aston Villa.

Hakan na nufin De Bruyne ba zai buga wasa 10 ba cikin har da na gasar zakarun Turai tsakaninsu da Borussia Monchengladbach a ranar 24 ga watan Fabarairu.

"Likitan ya bayyana cewa bayan duba hoton raunin Kevin, zai yi jinyar mako hudu zuwa shida," in ji Guardiola.

Kocin ya kara da cewa "Abun takaici ne gare mu da shi kansa, saboda lamarin babu dadi."