Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool: Shin ta ɓare wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar ne?
A karon farko cikin kusan shekara hudu Liverpool ta yi rashin nasara a Anfield inda Burnley ta doke ta da ci daya mai ban haushi.
Wannan karawa da kungiyoyin biyu suka yi ranar Alhamis ta kawo karshen wasa 68 da Liverpool ta yi ba a ci ta ba.
Kafin wannan lokaci, kungiyar ta kwashe kwana 1,370 babu wanda ya doke ta a gidanta, a wani kayataccen tarihi da ta kafa.
Kocin kungiyar Jurgen Klopp ya dauki alhakin wannan rashin nasara ta Liverpool.
Liverpool - wadda ta dauki kofin gasar Premier a karon farko cikin shera 30 - tana fuskantar koma baya a wannan kakar wasannin, domin kuwa yanzu tana matsayi na hudu da maki shida tsakaninta da ta daya Manchester United.
Wani koma baya da kungiyar ta fuskanta a wannan kakar shi ne wasanni biyar da ta buga ba ta yi nasara ba, rabon ta da cin wasa tun 19 ga watan Disamba da ta ci Crystal Palace 7-0.
"An sha wuya a wannan wasan, da wahala a fadi yadda aka ji," Klopp ya shaida wa BBC. "Wadannan yaran kamar ba su ba ne suka ci 7-0 a baya, idan muna so mu ci gaba da irin wannan nasarar sai mun kara dagewa. Sun yi kokari a wasan Burnley amma an gaza samun nasara," in ji shi.
A ina matsalar Liverpool take?
Rashin nasarar farko da Liverpool ta yi a gida cikin kwana 1,370 da suka gabata bayan wadda ta yi a hannun Palace a watan Afrilun 2017, amma a wannan karon an doke su bayan da Ashley Barnes ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Shi ne cinyewa ta farko da aka yi musu cikin wasa 69, wannan ne dogon lokacin na biyu da wata kungiyar ta dauka ba a doke ta ba gida, bayan wanda Chelsea ta yi a wasa 86 kafin a doke ta a watan Oktoban 2008.
Duk da cewa suna da masu fama da ciwo kamar Virgil van Dijk da Joe Gomez, amma matsalarsu ta bayyana a cikin filin wasan da suke casa mutane.
Tun lokacin da Sadio Mane ya ci kwallo a wasan West Brom da suka yi 1-1 a ranar 27 ga watan Disamaba, Liverpool ta kai 87 a Premier, ciki har da 27 da suka buga a wasan Burnley.
Klopp, wanda ya bar 'yan wasan gabansa biyu a benci Mohamed Salah da Roberto Firmino har sai minti 57 da ya sa su, ya shaida wa BBC cewa "Laifina ne kuma haka abin yake. Dole mu dauki matakin da muke ganin zai yi daidai, dole mu rika yin abin da ya dace kodayaushe."