Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta dage kan Koulibaly, Atletico na son Kondogbia
Liverpool ba ta hakura ba da ɗan wasan baya na Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, yayin da take son ƙara ɗinke bayanta. (Daily Star)
Carlo Ancelotti ya jaddada cewa matashin ɗan wasan gaba mai shekara Moise Kean zai dawo taka leda a kakar baɗi a Everton bayan bayar da shi aro zuwa Paris St-Germain finishes. (Liverpool Echo)
Barcelona za ta sake taya ɗan wasan Manchester City Eric Garcia mai shekara 19 idan an buɗe kasuwar ƴan wasa a Janairu. (ESPN)
Kocin Bayern Munich Hansi Flick yana da tattabaci kan ɗan wasan Austria David Alaba, mai shekara 28, zai sabunta kwangilar shi da kulub ɗin. (Goal)
Ɗan wasan Wales da Tottenham Gareth Bale ya bayar da tallafin fan £15,000 domin taimakawa mabukata a Wales. (Wales Online)
Daraktan gudanarwar Arsenal Huss Fahmy zai bar kulub ɗin bayan shekara uku a kulub ɗin. (Standard)
Fitaccen dillalin ƴan wasa Mino Raiola ya isa AC Milan domin tattauna batun sabunta kwangilar golan kulub ɗin Gianluigi Donnarumma, mai shekara 21, da ɗan wasan baya Alessio Romagnoli, mai shekara 25. (Football Italia)
Atletico Madrid na son ɗan wasan Valencia da Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya Geoffrey Kondogbia, mai shekara 27. (Le10Sport)
Sheikh Khaled bin Zayed Al Nehayan, zai saye kulub ɗin Derby County wanda ɗan uwa ne ga mai Manchester City Sheikh Mansour. (Telegraph- subscription required)
Ɗan wasan tsakiya Bannan zai sabunta kwangilar shi da Sheffield ɗan wasan mai shekara 30 ya ce zai ci gaba da taka leda ko da ƙungiyar ta fita gasar Premier. (Yorkshire Post)