Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Kabak, Wilshere, Romero, Pochettino, McGurk da White

Liverpool ta fara tattaunawa da ƙungiyar Schalke ta Jamus kan sayen ɗan wasan bayanta ɗan ƙasar Turkiyya Ozan Kabak mai shekara 20 bayan raunin da mai tsaron bayanta ɗan Netherlands Virgil van Dijk.(Sunday Mirror)

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Jack Wishire, mai shekara 28 ya fi son komawa Amurka domin buga wasa a gasar MLS bayan da ya bar ƙungiyar West Ham.(Sunday Mirror)

Mai tsaron gidan Manchester United kuma dan Argentina Sergio Romero na shirin tattaunawa kan barin Old Trafford. Mai shekara 33 na fatan za a cimma yarjejeniya da kungiyar bayan da aka sanar da ba a bukatarsa a shafukan sada zumunta. ((Star on Sunday)

Real Marid ta tuntubi tsohon kocin Tottenham da Southamptom Mauricio Pochettino kan ko zai maye gurbin Zinedine Zidane. (El Transistor)

Leeds na son sake dauko dan wasan tsakiya na Wigan mai shekara 17 wato Sean McGurk, bayan da aka kasa cimma matsaya a watannin baya (Sun)

Kocin Brighton Graham Potter ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yi cewa dan wasan baya Ben White mai shekara 23 zai koma Liverpool. Ya ce surutu ne kawai. (Sunday Mirror)

Tsohon dan wasan baya na kungiyar Brighton Mark Lawrenson wanda yanzu yake aiki da BBC ya ce Ben White na iya bin sahunsa ya koma Liverpool ama ba ya jin Zakarun Gasar Firimiyan za su neme shi a watan Janairu mai zuwa. (Argus)

Kocin Fulham Scott Parker ya yarda cewa mukaminsa na kocin na rawa bayan da aka ci kungiyar har sau biyar a Gasar Firimiya. (Sky Sports)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya bukaci shugaban kungiyar Daniel Levy ya goyi bayansa wajen sauya kungiyar ta hanyar sayen sabbin 'yan wasa kamar yadda Liverpool tayi a 'yan shekarun nan. (Sunday Express)

Wolves, West Ham, Crystal Palace, Southampton da Newcastle na nuna sha'awarsu kan dan wasan Reading Liam Moore mai shekara 27. (TeamTalk)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya tabbatar wa dan wasan tsakiya na kungiyar Donny van de Beek mai shekara 23 kuma dan Netherlands cewa ya ci gaba da hakuri lokacinsa na zuwa. (Manchester Evening News)

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce sayar da dan wasan gaba na kungiyarsa Rhian Brewsrer mai shekara 20 da yayi wa Sheffield United "abu ne da ya dame shi". (Sunday Express)