Cristiano Ronaldo yana ta cin kwallaye, Real Madrid na cikin matsala

Ranar Laraba Juventus ta lashe Italian Super Cup, bayan da ta yi nasara a kan Napoli da ci 2-0.

Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallon farko kuma na 760 da ya ci a tarihin sana'arsa ta tamaula.

Kuma kwallo na 32 a wasa 32 da ya buga wa Juventsu, shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Serie A ta bana mai 15 a raga.

Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Juventus a Julin 2018, bayan wasa 268 da ya buga a Spaniya da cin kwallo 311.

Real Madrid ta yi bankwana da Copa del Rey na bana kwana shida tsakani da aka doke ta a Spanish Super Cup.

Alcoyano ce ta yi waje road da Real da ci 2-1 a karawar kungiyoyi 32 da suka rage a wasannin.

Real Madrid na fuskantar kalubale a kakar bana, bayan da ba ta sayi dan kwallo ko day aba.

Real din na kasa cin kwallaye, sannan tana kasa doke kananan kungiyoyin da ta hadu da su a bana.

Kungiyar ta Spaniya tana da masu ci mata kwallaye da suka hada da Vinicius da Lucas Vazquez da Mariano da Eden Hazard da Marco Asensio da kuma Karim Benzema.

Sai dai koci Zinedine Zidane ya mayar da hankalinsa ga Benzema da cewar shi ne zai iya fitar da kungiyar kunya.

Kuma shi kansa dan wasan tawagar Faransa kwallo takwas ya ci a gasar La Liga, kuma shi ne kan gaba a Real Madrid.

Hakan ne ke nuna cewar lallai Real Madrid na kamfar cin kwallaye a bana, shi kuwa Cristiano Ronaldo sai zura su yake a raga a Juventus.

Yanzu dai kofi biyu Real ke son dauka a bana da ya hada da na La Liga da na Champions League.