Juve ta ja ragamar rukuni na bakwai a Champions League, bayan doke Barca 3-0

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Juventus ta ja ragamar rukuni na bakwai a gasar Champions League, bayan da ta doke Barcelona da ci 3-0 a Camp Nou ranar Talata.

Juventus ta fara cin kwallo a bugun fenariri ta hannun Cristiano Ronaldo minti na 13 da fara wasa, sannan ta kara na biyu a minti bakwai tsakani ta hannun Weston McKennie.

Bayan da kungiyoyin suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Juventus ta kara na uku ta hannun Cristiano Ronaldo kuma a bugun fenariti.

Da wannan sakamakon Juventus ta zama ta daya a rukuni na bakwai da maki 15, itama Barcelona maki 15 ne da ita a mataki na biyu.

A wasan farko da suka kara a bana a cikin rukuni, Barcelona ce ta yi nasara a kan Juventus da ci 2-0 a Italiya.

Karawa hudu baya da suka yi: Kafin sakamakon wasan Talata da Juventus ta yi nasara, Barcelona ta buga wasa hudu ba tare da an doke ta ba a fafatawa hudu da Juventus, inda ta ci biyu da canjaras biyu a Champions League, ta kuma ci karawa biyu daga ukun da suka yi a cikin rukuni da canjaras daya.

Karawarsu a Camp Nou: Juventus ta yi nasara a wasa biyu a Camp Nou a Champions League shi ne wanda ta ci 2-1 a Afirilun 2003 da kuma 4-0 a Disambar 2020 daga lokacin ta yi canjaras daya da rashin nasara a karawa daya wato 0-0 a 2016/17 aka kuma doke ta 0-3 a kakar 2017/18.

Wasannin cikin rukuni: Juventus ta yi nasara a wasa 10 daga 11 da ta kara a Champions League a cikin rukuni, rashin nasarar da ta yi ita ce wadda Barcelona ta doke ta 2-0 a kakar bana kuma a Italiya.

Cristiano Ronaldo da Barcelona: Cristiano Ronaldo ya ci Barcelona kwallo 17 a wasa 21 da ya fuskanci kungiyar a dukkan fafatawa.

'Yan wasan Barcelona da suka fuskanci Juventus:

Masu tsaron raga: Marc-Andre ter Stegen da Neto da kuma Inaki Pena.

Masu tsaron baya: Sergino Dest da Clement Lenglet da Ronald Araujo da Samuel Umtiti da Oscar Mingueza, da kuma Jordi Alba.

Masu buga tsakiya: Frenkie de Jong da Sergio Busquets da Miralem Pjanic da Riqui Puig da Carles Alena da Philippe Coutinho da Pedri da Matheus Fernandes.

Masu cin kwallaye: Martin Braithwaite da Lionel Messi da Antoine Griezmann da Francisco Trincao da kuma Konrad de la Fuente.

'Yan wasan Juventus dasuka fafata da Barcelona:

Masu tsaron raga: Szczesny da Pinsoglio da kuma Buffon.

Masu tsaron baya: De Light da Alex Sandro da Danilo da Cuadrado da Bonucci da Dragusin da kuma Frabotta.

Msu buga tsakiya: Arthur da ERamsey da McKennie da Chiesa da Rabiot da Bentancur da Bernardesci da Portanova da kuma Kulusevski.

Masu cin kwallo: Ranaldo da Morata da Dybala da kuma Da Graca.

Wasannin da Barcelona za ta buga zuwa jkarshen Disamba:

Ranar Lahadi 13 ga watan Disamba La Liga

  • Barcelona da Levante

Ranar Laraba 16 ga Disamba La Liga

  • Barcelona da Sociedad

Asabar 19 ga watan Disamba La Liga

  • Barcelona da Valencia

Talata 22 ga watan Disamba La Liga

  • Valladolid da Barcelona

Talata 29 ga watan Disamba La Liga

  • Barcelona da Eibar

Wasannin da Juventus za ta fafata zuwa karshen Disamba:

Ranar 13 ga watan Disamba Serie A

  • Genoa da Juventus

Ranar Laraba 16 ga watan Disamba Serie A

  • Juventusda Atalanta

Ranar Asabar 19 ga watan Disamba Serie A

  • Parma da Juventus

Ranar Talata 22 ga watan Disamba Serie A

  • Juventus da Fiorentina