Abubuwan da za su faru a Champions League Talata da Laraba

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata za a buga wasa na shida-shida a cikin rukuni a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League.
A ranar za a yi wasa takwas tun daga rukuni na biyar da na shida da na bakwai da kuma na takwas, domin samun kungiyoyin da za su kai zagaye na biyu a gasar.
Ga jerin wadanda ake ganin za su iya samun gurbin zagaye na biyu a Gasar ta Zakarun Turai ta bana.
Rukunin farko: Atletico ko kuma Salzburg
Rukuni na biyu: Mönchengladbach ko Shakhtar ko Real Madrid ko kuma Inter Milan
Rukuni na hudu: Atalanta ko kuma Ajax
Rukuni na shida: Lazio ko kuma Club Brugge
Rukuni na takwas: Manchester United da Paris Saint-Germain da kuma Leipzig
Wadanda za su yi na uku su koma buga Gasar Zakarun Turai ta Europa League ta kungiyoyi 32
Rukuni na biyar: Krasnodar
Wadanda ba za su kai zagaye na biyu ba sai dai su karkare a mataki na uku a cikin rukuni
Rukunin farko: Lokomotiv Moskva
Rukuni na uku: Olympiacos ko kuma Marseille
Rukuni na bawai: Dynamo Kyiv ko kuma Ferencváros
Wadanda za su kare a mataki na hudu na karshe a cikin rukuni
Rukuni na hudu: Midtjylland
Rukuni na biyar: Rennes
Rukuni na shida: Zenit St Petersburg
Rukuni na takwas: İstanbul Basaksehir
Sai dai kuma hakan zai faru ne idan kungiyoyin sun kammala wasannin karshe na cikin rukuni.
Wasannin da za a buga ranar Talata 8 ga watan Disamba
Rukuni na biyar:
Chelsea (maki 13) da Krasnodar (maki 4)
Rennes (maki 1) da Sevilla (maki 10)
Chelsea ta kai zagaye na biyu a matakin ta daya a rukunin.
Sevilla ce ta biyu a wannan rukunin itama ta kai karawar zagaye na biyu.
Krasnodar za ta kare a mataki na uku ta fada UEFA Europa League na kungiyoyi 32.
Rennes za ta karkare a mataki na hudu ta karshe a rukunin.
Rukuni na shida:
Lazio (maki 9) da Club Brugge (maki 7)
Zenit (maki 1) da Dortmund (maki 10)
Dortmund ta kai mataki na biyu za kuma ta ja ragamar rukunin da zarar ta doke Zenit, idan kuma sun tashi canjaras, sakamakon karawar Lazio da Club Brugge za ta tantance wadda za ta yi ta daya da ta biyu.
Lazio za ta kai zagaye na biyu idan Club Brugge ba ta doke ta ba. Za ta iya zama ta daya idan ta yi nasara, Dortmund ta kasa cin wasanta, ko kuma Lazio ta yi canjaras a doke Dortmunf.
Club Brugge za ta kai karawar zagaye na biyu idan ta yi nasara a kan Lazio.
Zenit ce za ta karkare a mataki na hudu a wannan rukunin.
Rukuni na bakwai:
Barcelona (maki 15) da Juventus (maki 12)
Dynamo Kyiv (maki 1) da Ferencvaros (maki 1)
Barcelona da Juventus sun kai wasan zagaye na biyu, kuma Juventus za ta zama ta daya idan ta ci Barca kwallo uku ko fiye da haka, ko kuma ta yi nasara da ci 2-0 a Camp Nou.
Dynamo da Ferencvaros ba za su kai zagaye na biyu ba, kuma Dynamo na bukatar sakamako kamar 0-0 ko 1-1 ko kuma 2-2 ko makamancin hakan, idan hakan bai yiwuba Ferencvaros ta zama ta uku.
Rukuni na takwas:
Paris Saint-Germain (maki 9) da İstanbul Basaksehir (maki 3)
Leipzig (maki 9) da Manchester United (maki 9)
Manchester United za ta kai zagayen gaba idan ba ta yi rashin nasara a Leipzig ba. United za ta ja ragama da zarar Leipzig ba ta doke ta ba, idan kuma PSG ta kasa nasara a kan Basaksehir.
Paris za ta kai karawar gaba idan Basaksehir ba ta doke ta ba kuma ko ta yi rashin nasara za ta kai karawar gaba idan daya sakamakon ba su tashi canjaras ba. PSG za ta yi ta daya idan ta ci wasanta.
Leipzig za ta kai zagayen gaba idan ta doke United, ko suka tashi canjaras da zarar PSG tasha kashi a hannun Basaksehir. Leipzig za ta ja ragamar rukunin idan ta yi nasara aka doke PSG a daya wasan.
İstanbul Basaksehir za ta kare a matakin karshe a rukuni na takwas.











