Kano Pillars: An yi wajerod da ƙungiyar daga gasar CAF Confederation Cup

Asalin hoton, Kano Pillars
An yi wajerod da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars daga gasar zakaru ta CAF Confederation Cup a jiya Asabar bayan ta tashi wasa 0-0 da A.S.C Jaraaf ta ƙasar Senegal.
Masu Gida sun fice daga gasar ne sakamakon sun kasa rama 3-1 da aka ɗura musu a Senegal ranar 27 ga Nuwamba.
An buga wasan ne a filin wasa na Ahmadu Bello da ke garin Kaduna a yammacin Asabar, inda aka doke ta 3-1 wasa gida da waje.
Ita ma ƙungiyar Plateau United ta fice daga Gasar Zakarun Afirka ta CAF Champions League bayan ta tashi wasa 0-0 da Simba Sports Club a ƙasar Tanzania.
A wasan farko da suka buga a Najeriya, Plateau United ta sha kashi da 0-1. An doke ta 1-0 a wasa gida da waje kenan.
Ita ma Rivers United kashi ta sha a hannun Futuro Kings da 2-1 a gasar CAF Confederation Cup har gida.
Ƙungiyar Enyimba ce kaɗai ta ci wasanta na farko 1-0 a gasar Zakarun Afirka daga Najeriya, inda ta doke Rahimo FC 1-0 a Najeriya kuma ranar Lahadi za su fafata a wasa na biyu.
Ita ma Rivers za ta buga wasa na biyu da Futuro Kings a Lahadin a Equatorial Guinea.











