Sadio Mane ya ci wa Senegal kwallo a wasa da Guinea-Bissau

Sadio Mane

Asalin hoton, Getty Images

Senegal na daf da samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2022, bayan da ta doke Guinea-Bissau da ci 2-0 ranar Laraba.

Mane, wanda bai buga wa Senegal wasan sada zumunta ba a watan jiya, sakamakon kamuwa da cutar korona, shi ne ya fara cin kwallo a a bugun fenariti.

Senegal ta ci na biyu ne ta hannun Opa Nguette, bayan da ya shiga karawar daga baya, kuma hakan ya bai wa tawagar hada maki uku a rukunin.

A wani wasan kuma da aka yi ranar Larabar, Comoros ta buga 1-1 da Kenya a Nairobi duk da an korar mata dan wasa daya a fafatawar.

Tsibirin Comoros mai mutum kasa da miliyan daya ya fara buga manyan wasanni a 2006, wanda kawo yanzu yake taka rawar gani musamman da manyan kasashe.

Youssouf M'Changama ya fara cin kwallo a minti na 26, daga baya aka mai jan kati, bayan karbar katin gargadi biyu har da na bata lokacin wasa kuma tun kan hutu.

A minti na 65 Kenya ta farke ta hannun Masud Juma, kuma canjaras na uku a jere da kasar ta yi a rukuni na bakwai.

Ita kuwa Comoros wacce har yanzu ba a doke ta ba a rukunin na fatan kai wa gasar cin kofin nahiyar Afirka a karon farko, wanda Kamaru za ta karbi bakuncio a 2022.

Kungiyoyi bibiyu ne daga kowanne rukuni 12 za su wakilci nahiyar a gasar kofin Afirka, in banda rukuni na shida da za a zabi biyu banda Kamaru dake cikinsu.