Joe Gomez: Zai yi jinya zuwa karshen kakar shekarar 2020/21

Joe Gomez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gomez ya buga wa Liverpool karawar da ta tashi 1-1 da Manchester City ranar Lahadi a Etihad.

Watakila mai tsaron bayan Liverpool, Joe Gomez ya yi jinya har zuwa karshen kakar bana kamar yadda kungiyar ta sanar.

Gomez ya yi rauni ne a lokacin da yake atisaye a tawagar Ingila a shirin da take na buga wasan sada zumunta da Jamhuriyar Ireland ranar Alhamis.

Liverpool ta ce likitoci sun yi wa dan wasan mai shekara 23 aiki cikin nasara a raunin da ya yi a gwiwar kafarsa ta hagu.

Liverpool na fama da 'yan wasanta masu tsaron baya da ke jinya a kakar 2020/21.

Cikinsu har da Virgil van Dijk wanda shima ke jinya mai tsawo kafin ya dawo taka leda nan gaba.

Van Dijk ya yi rauni ne a lokacin da Liverpool ke buga wasa da Everton da suka tashi 2-2 ranar 17 ga watan Oktoba.

Mai rike da kofin Premier League na fama da Fabinho shima dake jinya, wanda ke tsaron baya tare da Van Dijk a lokacin tamaula.

Haka kuma kungiyar ta damu da raunin mai tsaron bayanta Trent Alexander-Arnold, wanda aka sauya shi a karawar Premier League da suka tashi 1-1 da Manchester City ranar Lahadi.

Hakan ne ya sa tawagar kwallon kafa ta Ingila ba ta gayyace shi wasan sada zumunta da Ireland ba ranar Alhamis da wanda za ta fafata da Iceland a Nations League ranar 18 ga watan Nuwamba ba.

Liverpool tana ta uku a kan teburin Premier da maki 17, bayan da Leicester ce ke jan ragama da maki 18, sai Tottenham ta uku mai maki iri daya da na Liverpool.