'Yan Madrid da aka gayyata don yi wa kasarsu wasa

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Kimanin 'yan wasan Real Madrid 12 ne tawagogin kasarsu suka gayyace su domin buga musu tamaula tun daga ranar Laraba.

'Yan wasan sun hada da Ramos da Asensio da Varane da Kroos da Courtois da Modric da Odegaard da Lunin da Jovic da Vinicius Jr. da Valverde da kuma Rodrygo.

Shi dai Rodrygo zai buga wa tawagar Brazil ta Olympic wasannin sada zumunta biyu.

'Yan wasan ko dai za su buga fafatawar sada zumunta ko ta Nations League ko kuma ta neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Ga jerin 'yan kwallon da wasannin da za su fafata:

Tawagar kwallon kafa ta Spaniya ta kira Ramos da kuma Asensio don buga mata wasanni kamar haka

  • Ranar Laraba Netherlands-Spain
  • Ranar Asabar Switzerland-Spain
  • Ranar Talata Spain-Germany

Shi kuwa Varane zai yi wa tawagar Faransa wasanni uku da suka hada da

  • Ranar Laraba France-Finland
  • Ranar Asabar Portugal- France
  • Ranar Talata France-Sweden

Mai taron ragar Real Madrid, Courtois zai wakilci Belgium a wasan da za ta yi kamar hada

  • Ranar Laraba Belgium-Switzerland
  • Ranar Lahadi Belgium-England
  • Ranar Laraba Belgium-Denmark

Shi kuwa Luca Modric zai buga wasa uku da Croatia za ta fafata

  • Ranar Laraba Turkey-Croatia
  • Ranar Asabar Sweden-Croatia
  • Ranar Talata Croatia-Portugal

Tawagar kwallon kafa ta Jamus ta gayyaci Toni Kross don yi mata wasa uku

  • Ranar Laraba Jamus-Jamhuriyar Czech
  • Ranar Asabar Jamus-Ukraine
  • Ranar Talata Spain-Jamus

Shi kuwa Odegaard zai buga wa tawagar Norway wasanni shima ukun

  • Laraba Norway-Israel
  • Ranar Lahadi Romania-Norway
  • Ranar Laraba Austria-Norway

Luka Jovic kuwa zai yi wa Serbia wasa uku ne

  • Ranar Alhamis Serbia-Scotland
  • Ranar Lahadi Hungary-Serbia
  • Ranar Laraba Serbia-Russia

Ita kuwa Ukraine ta gayyaci Lunin domin fuskantar wasa uku

  • Ranar Laraba Poland-Ukraine
  • Ranar Asabar Germany-Ukraine
  • Ranar Talata Switzerland-Ukraine

Shi kuwa Vinicius karawa biyu zai buga wa tawagar Brazil a wasan neman shiga gasar kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci

  • Ranar Asabar Brazil-Venezuela
  • Ranar Laraba Uruguay-Brazil

Rodrygo kuwa zai buga wa tawagar Brazil ta Olympic wasan sada zumunta da za ta yi a Saudi Arabia da kuma wanda za ta fafata a Masar

  • Ranar Asabar Tawagar Brazil ta Olympic da Tawagar Koriya ta Kudu ta Olympic
  • Ranar Talata Tawagar Brazil ta Olympic da Tawagar Masar ta Olympic