Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan Madrid da aka gayyata don yi wa kasarsu wasa
Kimanin 'yan wasan Real Madrid 12 ne tawagogin kasarsu suka gayyace su domin buga musu tamaula tun daga ranar Laraba.
'Yan wasan sun hada da Ramos da Asensio da Varane da Kroos da Courtois da Modric da Odegaard da Lunin da Jovic da Vinicius Jr. da Valverde da kuma Rodrygo.
Shi dai Rodrygo zai buga wa tawagar Brazil ta Olympic wasannin sada zumunta biyu.
'Yan wasan ko dai za su buga fafatawar sada zumunta ko ta Nations League ko kuma ta neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Ga jerin 'yan kwallon da wasannin da za su fafata:
Tawagar kwallon kafa ta Spaniya ta kira Ramos da kuma Asensio don buga mata wasanni kamar haka
- Ranar Laraba Netherlands-Spain
- Ranar Asabar Switzerland-Spain
- Ranar Talata Spain-Germany
Shi kuwa Varane zai yi wa tawagar Faransa wasanni uku da suka hada da
- Ranar Laraba France-Finland
- Ranar Asabar Portugal- France
- Ranar Talata France-Sweden
Mai taron ragar Real Madrid, Courtois zai wakilci Belgium a wasan da za ta yi kamar hada
- Ranar Laraba Belgium-Switzerland
- Ranar Lahadi Belgium-England
- Ranar Laraba Belgium-Denmark
Shi kuwa Luca Modric zai buga wasa uku da Croatia za ta fafata
- Ranar Laraba Turkey-Croatia
- Ranar Asabar Sweden-Croatia
- Ranar Talata Croatia-Portugal
Tawagar kwallon kafa ta Jamus ta gayyaci Toni Kross don yi mata wasa uku
- Ranar Laraba Jamus-Jamhuriyar Czech
- Ranar Asabar Jamus-Ukraine
- Ranar Talata Spain-Jamus
Shi kuwa Odegaard zai buga wa tawagar Norway wasanni shima ukun
- Laraba Norway-Israel
- Ranar Lahadi Romania-Norway
- Ranar Laraba Austria-Norway
Luka Jovic kuwa zai yi wa Serbia wasa uku ne
- Ranar Alhamis Serbia-Scotland
- Ranar Lahadi Hungary-Serbia
- Ranar Laraba Serbia-Russia
Ita kuwa Ukraine ta gayyaci Lunin domin fuskantar wasa uku
- Ranar Laraba Poland-Ukraine
- Ranar Asabar Germany-Ukraine
- Ranar Talata Switzerland-Ukraine
Shi kuwa Vinicius karawa biyu zai buga wa tawagar Brazil a wasan neman shiga gasar kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci
- Ranar Asabar Brazil-Venezuela
- Ranar Laraba Uruguay-Brazil
Rodrygo kuwa zai buga wa tawagar Brazil ta Olympic wasan sada zumunta da za ta yi a Saudi Arabia da kuma wanda za ta fafata a Masar
- Ranar Asabar Tawagar Brazil ta Olympic da Tawagar Koriya ta Kudu ta Olympic
- Ranar Talata Tawagar Brazil ta Olympic da Tawagar Masar ta Olympic