Kasuwar 'yan wasa: Makomar Brenner, da Grealish, da Ronaldo, da Pogba

Paris St-Germain na shirin taya dan wasan Portugal da Juventus Christiano Ronaldo idan har kulob din da yake a kasar Italiya ya ce zai sayar da shi. (Mail)

PSG din kuma na tattaunawa da dan wasanta na gaba Neymar, inda ake ganin dan wasan mai shekara 28 zai iya sanya hannu kan kwantaragin da zai kai shi shekara biyar masu zuwa a kulob din. (ESPN)

Arsenal na daya daga cikin kulob na gaba-gaba da ke son dauko dan wasan Sao Paulo, Brenner mai shekara 20. (Calciomercato - in Italian)

Tsohon dan wasan Liverpool Jamie Carragher na daga cikin wadanda ke ganin ya kamata Manchester United ta sayar da dan wasanta Paul Pogba. (Talksport)

Da alama cewa Manchester United za ta iya taya dan wasan Aston Villa Jack Grealish idan har Pogba ya kungiyar ta Manchester United. (Manchester Evening News)

Saura kirin Arsenal ta sayi dan wasan Jude Bellingham na Borussia Dortmund a shekara ta 2019 lokacin yana taka leda a Birmingham City. (Sky Sports, via Independent)

Arsenal din kuma ta fara taya dan wasan Red Bull Salzburg mai shekara 20, Dominik Szoboszlai kan kudi fan miliyan 22. (Football London)

Leicester City ta fara tattaunawa domin bai wa dan wasan bayanta Johny Evans sabuwar kwantaragi. Yanzu haka yana gab da shiga shekarar karshe ta kwantaraginsa ta shekara 3. (Athletic - subscription required)

Dan wasan tsakiya na Netherlands Donny van de Beek zai so ya rinka buga wa kungiyarsa ta Manchester United wasa sosai, sai dai kocin kasarsa Frank de Boer na ganin cewa sai ya yi matukar kokari kafin ya samu damar shiga tsara a 'yan wasan tsakiya na kungiyar. (Sun)

Dan wasan gefe na kungiyar Arsenal Nicolas Pepe ya bayyana rashin jin dadin sa game da rashin ba shi isasshen lokaci na taka leda a kungiyar. (Canal Plus, via Mirror)