Makomar Haaland da Ndombele da Saliba da Diaby da Alaba

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge, ya ce yana son mai tsaron baya David Alaba ya ci gaba da zaman ƙungiyar, amma shawara ta rage ga ɗan wasan mai shekara 28. (Bild - in German)
Real Madrid na son ƙulla yarjejeniya da Alba idan kwantiraginsa ta ƙare a kakar gaba. (Diario AS, via Mail)
Ɗan wasan gaban Norway Erling Haaland, mai shekara 20, babu inda aka ambato ko ba shi da damar sauya sheƙa kafin cikar wa'adin kwantiraginsa, a cewar shugaban Borussia Dortmund Hans-Joachim Watzke. (Bild - in German)
Barcelona na iya tayin ɗauko ɗan wasan tsakiya a Tottenham dan asalin Faransa Tanguy Ndombele, mai shekara 23, a kaka mai zuwa. (Fabrizio Romano)
Kocin Arsenal Mikel Arteta, ya ce William Saliba mai shekara 19 ɗan Faransa, na iya zuwa wani kulob din a matsayin aro a watan Janairu. (Mail)
Mai tsaron baya a Ajax da Mexico Edson Alvarez, mai shekara 23, ya bayyana sha'awarsa da burin ganin wata rana ya taka leda a Manchester City.(Voetbalzone, via Goal)
Manchester United ta rasa damar cimma yarjejeniya da ɗan wasan Bayer Leverkusen, da ke buga gefe Moussa Diaby ɗan Faransa, mai shekara 21, a kasuwar cinikin ƴan wasa a bazara. (Bild, via Mail)
Ɗan wasan gaba a Manchester United Mason Greenwood, mai shekara 19, ana saran komawarsa Ingila a ranar Alhamis. (Guardian)
Kocin Arsenal Arteta bai shirya cewa uffan ba kan tsawaita kwantiragin ɗan wasan tsakiya mai shekara 28 Mohamed Elneny na Masar, wanda ke ƙarewa a ƙarshen kaka. (Goal)
An soma tattaunawa tsakanin mai tsaron baya Sergio Ramos ɗan Spaniya da ƙungiyarsa ta Real Madrid kan ƙulla sabon kwantiragi. (ESPN)
Hukumar firimiyar Ingila za ta tattauna da ƴan jaridu kan sabbin tsarin biyan kuɗaɗe bayan tattaunawa da ƙungiyoyin wasannin firimiya 20 a ranar Alhamis. (Telegraph)
Tsohon ɗan wasan gaba a Aston Villa Gabriel Agbonlahor, ya ce sabuwar yarjejeniyar da za a cimma da ɗan wasan tsakiya dan asalin Scotland, John McGinn, mai shekara 26 na iya kafa tarihi a kulob ɗin. (Football Insider)
Mai ƙungiyar Leeds United Andrea Radrizzani, mai shekara 46 ya ce a shirye yake ya bunƙasa ƙungiyar, kamar irin yadda aka gani a Red Bull da rukunin City Football, masu kulob ɗin Manchester City. (Yorkshire Evening Post)











