El Clasico: Karon farko da Barcelona da Real Madrid za su kara a 2020-21

El Clasico

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Za a buga wasan hamayya tsakanin Barcelona da Real Madrid a gasar La Liga ranar 24 ga watan Oktoba, wasan farko da za su fafata a bana.

Wannan shi ne wasan farko da za a fafata tsakanin Ronald Koeman da Zinedine Zidane a matsayin masu horar da tamaula.

Koeman, dan kasar Netherland, ya karbi aikin jan ragamar Barcelona bayan da ta sallami Quique Setien, wanda ya kasa taka rawar gani a kakar da ta wuce.

A bara da kungiyoyin suka fafata a Camp Nou sun tashi karawar ba ci wato 0-0 a karkashin koci Ernesto Valverde.

El Clasico

Asalin hoton, Getty Images

Rabonda Real Madrid da Barcelona su fuskanci juna tun 1 ga watan Maris, a wasan da Real ta yi nasara da ci 2-0 a Santiago Bernabeu, inda Vinicius Junior da kuma Mariano Diaz suka ci kwallayen.

Kuma shi ne wasa na karshe da aka buga a Bernabeu daga nan cutar korona ta kawo koma baya aka dakatar da wasanni.

Hakan ne ya bai wa Madrid damar fara gyaran filin wasanta, inda ta koma buga karawa a wajen da take gabatar da atisaye wato filin Alfredo Di Stefano kawo yanzu.

Koda yake ana buga wasannin kakar ban aba 'yan kallo don gudun yada cutar korona.

Real Madrid za ta buga El Clasico, bayan ta yi wasa da Cadiz a gasar ta La Liga ranar 17 ga watan Oktoba, sannan ta buga wasan farko a gasar Champions League a gida da Shakhtar Donetsk ranar 21 ga watan Oktoba.

Ita kuwa Barcelona za ta fafata da Getafe a gasar ta La Liga ranar 17 ga watan Oktoba, sannan Barcelona ta karbi bakuncin Ferencvaros ranar 20 ga watan Oktoba a gasar ta Champions League.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 10, bayan wasa hudu da ta buga, yayin da Barcelona mai maki bakwai tana mataki na biyar bayan karawa biyu da ta yi.