Lionel Messi: Kyaftin ɗin tawagar Argentina ya ci mata ƙwallo 71 a tarihi

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata tawagar kwallon kafa ta Bolivia za ta kara da ta Argentina a wasa na biyu na cikin rukuni a karawar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Kasashen na buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
A wasan farko na cikin rukuni da suka kara ranar Juma'a, Argentina ta yi nasara ne a gida a kan Ecuador da ci 1-0, kuma Lionel Messi ne ya ci kwallo a bugun fenariti.
Rabon da Argentina ta buga wasa tun bayan wanda ta yi wasan sada zumunta da Uruguay a Tel Aviv cikin watan Nuwambar 2019, saboda tsoron yada cutar korona.
Kwallon da Messi ya ci Ecuador ya hada 71 jumulla da ya ci wa tawagar Argentina a wasa 139, kuma shi ne kan gaba a ci wa kasar kwallaye a tarihi.
Tun a cikin shekarar 2016 ya haura Gabriel Batistuta wanda ya ci wa tawagar Argentina kwallo 54.
Messi ya kusan kamo yawan buga wasa da tsohon dan kwallon Barcelona, avier Mascherano ya yi wa Argentina mai 147.
Haka kuma kyaftin din tawagar Barcelona shi ne na 11 a jerin wadanda ke kan gaba a zura wa tawagar kwallon kafa ta kasa kwallaye a tarihi.
Messi mai shekara 33 na neman cin kwallo shida nan gaba domin ya dara tarihin Pele na Brazil mai 77, idan kuma ya yi hakan shi ne zai zama kan gaba a cin kwallaye a nahiyar Kudancin Amurka.
Wadanda ke kan gaba a yawan ci wa tawaga kwallo a tarihi:











