Premier League: 'Yan wasan da ke kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga

Ole Gunnar Solskjare

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Ranar 17 ga watan Oktoba za a ci gaba da wasannin mako na biyar a gasar cin kofin Premier League ta 2020-21.

Kawo yanzu an buga wasa 38 an kuma ci kwallo 144, bayan kammala wasannin mako na biyar.

Kuma kawo yanzu Dominic Calvert-Lewin da kuma Son Heung-min su ne kan gaba wajen cin kwallaye a raga inda kowanne ke da shida-shida a raga.

Gasar ta Premier League ta bana na samun armashin cin kwallaye da dama, sai dai kuma masu bayar da kwallon da ake zura wa a raga su ne ke taka rawar gani a wasannin.

Duk da cewar wasa huɗu aka kara a kakar bana kawo yanzu, Harry Kane na Tottenham shi ne kan gaba da kwallo shida da ya bayar aka zura a raga a gasar shekarar nan.

Kuma ya yi namijin ƙoƙari a bana duk da cewar guda bakwai ya bayar da aka ci a kakar 2016-17, saboda haka yanzu aka fara lissafi.

Ko da yake ana ta buga wasannin bana ba 'yan kallo don gudun yaɗa cutar korona.

Jurgen klopp

Asalin hoton, Getty Images

Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasanni daga baya aka ci gaba ba 'yan kallo da ta kai aka ƙarƙare kakar bara wacce Liverpool ta lashe kofin kuma na farko tun bayan shekara 30.

A kakar da ta wuce Kevin De Bruyne shi ne kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga da 20 a kakar 2019/20, inda ya yi kan-kan-kan da Thierry Henry wanda ya fara bajintar a kakar Premier League.

Wasan da aka zazzaga kwallaye a Premier League ta bana a gida shi ne wanda Aston Villa ta doke Liverpool mai rike da kofi da ci 7-2 a wasan da suka fafata ranar 4 ga watan Oktoba.

A kuma ranar ce Tottenham ta je Old Trafford ta doke Manchester United da ci 6-1, kuma shi ne wanda wata kungiya ta je waje ta ci kwallaye da dama a bana.

'Yan wasan da ke kan gaba wajen bayar da kwallo a zura a raga a 2020/21

  • Harry Kane6
  • John McGinn3
  • Jack Grealish3
  • Daniel Podence2
  • Richarlison2
  • Willian 2
  • James Rodriguez2
  • Roberto Firmino2
  • Pablo Fornals2
  • Matheus Pereira2

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Premier ta bana:

  • Dominic Calvert-LewinEverton FC6
  • Heung-min Son Tottenham6
  • Mohamed Salah Liverpool5
  • Jamie Vardy Leicester City5
  • Callum Wilson Newcastle 4
  • Neal Maupay Brighton 4
  • James Rodriguez Everton FC3
  • Jorginho Chelsea3
  • Danny Ings FC Southampton3
  • Harry Kane Tottenham 3
  • Sadio Mane Liverpool3
  • Ollie Watkins Aston Villa3
  • Wilfried Zaha Crystal Palace FC3
  • Alexandre Lacazette Arsenal FC3
  • Jack Grealish Aston Villa3
  • Patrick Bamford Leeds United FC3

Wasannin mako na biyar:

Ranar 17 ga watan Oktoban 2020

  • Everton da Liverpool
  • Chelsea da Southampton
  • Manchester City da Arsenal
  • Newcastle United da Manchester United
  • Sheffield United da Fulham

Ranar 18 ga watan Oktoban 2020

  • Crystal Palace da Brighton & Hove Albion
  • Tottenham da West Ham United
  • Leicester City da Aston Villa

Ranar 19 ga watan Oktoban 2020

  • West Bromwich Albion da Burnley
  • Leeds United da Wolverhampton Wanderers