Alex Telles: Manchester United na daf da daukar dan wasan Porto

Alex Telles

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Telles ya koma Porto da taka leda daga Galatasaray a 2016

Manchester United na daf da kammala cinikin dan kwallon tawagar Brazil, mai wasa a Porto, Alex Telles.

Tun farko United ta yi jan kafa wajen sayen mai tsaron bayan mai shekara 27.

Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer na neman kara karfin mai tsaron baya daga hagu, ya kuma tabbatar Telles ne zai share masa kuka.

Porto na neman fam miliyan 18 daga United ga dan kwallon da yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar bana, wanda za a iya daukarsa a Janairu a matsayin mai cin gashin kai.

Telles wanda ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Brazil wasa daya tal, ya ci wa Porto kwallo 21 a wasa 127 da ya yi wa kungiyar.

Wannan labarin ya zo a lokacin da ake cewar United ta kusan kammala daukar Edison Cavani, wanda bai da kungiya tun bayan barin Paris St Germain.