Edinson Cavani: Manchester United na shirin sayen tsohon ɗan wasan PSG

Edinson Cavani playing for PSG

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cavani ya tafi PSG daga Napoli a shekarar 2013 kuma ya taimaka mata wurin lashe kofi shida na gasar Ligue 1
    • Marubuci, Daga Simon Stone
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport

Tsohon dan wasan Paris St-Germain Edinson Cavani zai tafi Ingila ranar Lahadin nan domin kammala yarjejeniyar komawa Manchester United.

Dan kasar Uruguay, mai shekara 33, ya dade yana tattaunawa da United kuma kodayake har yanzu ba su kulla yarjejeniya ba, amma rahotanni masu karfi sun nuna cewa Cavani zai sanya hannu kan kwangilar shekara biyu a United.

Cavani ba shi da kungiya tun da ya bar Paris St-Germain a karshen watan Yuni.

Ya bar PSG bayan samun rashin jituwa da Neymar inda ya ce yana ganin zai fi taka rawa a Ingila.

United ta samu kwarin gwiwa game da bukatar dan wasan ta murza mata leda kuma da zarar sun gana ido da ido, za a iya kulla yarjejeniya a tsakaninsu.

An fahimci cewa albashin da za a ba shi ba zai wuce wanda yake karba a baya ba, don haka United na ganin bai kamata a kwatanta shi da Alexis Sanchez ba, wanda ake biya £350,000 duk mako, amma ya gaza taka rawar gani.

Kazalika United na ganin shekarun Cavani ba wata matsala ba ce kuma kwarewarsa za ta taimaka wajen karfafa gwiwar matasan 'yan wasa a tawagar Ole Gunnar Solskjaer.

An fahimci cewa tattaunawar da United take yi domin dauko dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho ta cije, kodayake wasu majiyoyi a kungiyar sun ki bayar da tabbaci kan ko za ta daina zawarcin dan wasan na Ingila mai shekara 20

United ta shirya shan suka kan Cavani kodayake za ta kare kanta ta hanyar nuna irin bajintar da ya yi a baya.

Ya zura kwallaye 341 a wasanni 556 da ya murza. Ciki har da kwallo 200 da ya zura a matakin kungiya a wasanni 301 da ya buga wa PSG. Ya kuam ci kwallo 50 a wasannin kasasen duniya 116 da ya buga wa kasarsa Uruguay.