Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sancho, Jovic, Alaba, Tagliafico, Lamptey

Jadon Sancho

Asalin hoton, EPA

Borussia Dortmund ta yi watsi da tayin daManchester United ta yi mata na sayen dan wasan Ingila Jadon Sancho mai shekara 20 a kan £91.3m, a cewar Sky Sports.

Kazalika United tana tsoron wulakanciidan Dortmund ta sake yin fatali da tayin da za ta sake yi mata na sayen Sancho, in ji (Mail).

Sai dai a wani bangaren, United ta bi sahun wasu kungiyoyi da ke fafutukar dauko aron dan wasan Real Madrid da Serbia Luka Jovic, mai shekara 22. (AS - in Spanish)

Sannan ta kusa dauko dan wasan Barcelona da Faransa mai shekara 23 Ousmane Dembele - abin da zai bai wa Barca damar samun kudin dauko dan wasan Lyon Memphis Depay. (AS - in Spanish)

Kocin Manchester City Pep Guardiola yana son dauko dan wasan baya kafin a rufe kasuwar saye da musayar 'yan kwallo inda ake sa ran zai dauko dan wasan Bayern Munich da Austria David Alaba, da kuma dan wasan Ajax da Argentina Nicolas Tagliafico, dukkansu masu shekara 28. (Mail)

Bayern Munich ta tuntubi Brighton domin yiwuwar dauko dan wasan Ingila mai shekara 19 Tariq Lamptey. (Sport1, via Metro)

Southampton za ta iya neman dan wasan Heerenveen da Netherlands mai shekara 18 Joey Veerman. (Voetbal International, via TalkSPORT)

Wakilin Lucas Torreira ya isa Madrid domin tattaunawa da Atletico Madrid kan yiwuwar zuwan dan wasan na Uruguay kungiyar daga Arsenal.(Fabrizio Romano, via Express)

Chelsea ta amince ta sayar da dan wasan Jamus Antonio Rudiger kuma, kodayake Tottenham na sha'awar daukar dan wasan mai shekara 27, Chelsea ta fi so ya tafi kasashen waje. (ESPN)

Dan wasan Brazil Thiago Silva, mai shekara 36, ya ce ya ji "haushi" kan abin da Paris St-Germain ta yi masa game da barinsa kungiyar, kodayake kungiyar ta nemi tsawaita kwangilarsa da shekara daya, amma ta yi hakan ne bayan ya riga ya amince zai tafiChelsea. (ESPN)