Alex Telles: Man United na tattaunawa da Porto kan daukar dan wasan Brazil

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na tattaunawa da Porto kan batun daukar dan kwallon Brazil, Alex Telles.
Kocin United Ole Gunnar Solskjaer na fatan dinke barakar bayansa daga bangaren hagu, yana ganin dan wasan mai shekara 27 shi ne zai share masa kuka.
Porto na bukatar fam miliyan 18 ga dan kwallon wanda yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar bana, zai iya komawa wata kungiya a Janairu a matakin mai zaman kansa.
Telles wanda ya buga wa tawagar Brazil wasa daya, ya ci kwallo 21 a wasa 127 da ya yi wa Porto.
Solskjaer na fatan yin sauye-sauye a karawar da zai yi da Brighton ranar Laraba a Caraboa Cup, kwana hudu tsakani da United ta doke Brighton a gasar Premier League.
Har yanzu United ba ta hakura da zawarcin dan wasan Borussia Dortmund, Jadon Sanchoba ba da yake ranar 5 ga watan Oktoba za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai.







