David Wagner: Schalke ta kori mai horar da ita

An sallami tsohon mai horar da Huddersfield, David Wagner, bayan da aka doke Schalke wasa biyu a jere da fara gasar Bundesliga ta Jamus ta bana.

Rashin nasarar da kungiyar ta yi ya zama na 18 da Schalke ta kasa samun maki a gasar ta Bundesliga.

Kungiyar ta fara da yin rashin nasara da ci 8-0 a hannun Bayern Munich, sannan Werder Bremen ta doke ta 3-1 a wasan mako na biyu a gasar Bundesliga ranar Asabar.

Wagner, mai shekara 48, ya koma Schalke da horar da kwallo a 2019, bayan sama da kaka uku da ya ja ragamar Huddersfield a gasar Premier.

Wadanda ke aikin taimakawa kocin Christoph Buhler da kuma Frank Frohling duk sun bar Schalke din..