Barcelona: Lionel Messi, Luis Suarez da wasu sauran matsalolin

Barcelona na fuskantar matsaloli da dama a yayin da ta ke shirin buga wasan farko a La Liga a ranar Lahadi inda za ta karɓi bakuncin Villarreal - kuma kocin ƙungiyar, Unai Emery zai yi ƙoƙarin nuna tasirinsa a sabuwar ƙungiyarsa.

Yayin da Barcelona ke fuskantar ƙalubale, akwai wasu tambayoyi guda biyar game da Barcelona kamar yadda ta ke ƙokarin ƙaryata kallon da ake abubuwa sun taɓarɓare mata.

Ko Koeman na iya sauya ra'ayin Messi?

Abu ne mai wahala a yanzu a fara yin sharhi game da Barcelona kan wani abu da ya wuce batun Messi, bayan yunƙurin kaftin ɗin na barin Barcelona da kuma fushinsa kan shugaban ƙungiyar, Josep Maria Bartomeu da farin jininsa ya ragu.

A ranar Juma'a Messi ya nuna cewa har yanzu ba ya jin daɗi a Barcelona, yana mai nuna ɓacin rai a kalaman bankwana da ya yi wa abokin wasansa Luiz Suarez wanda koma Atletico Madrid.

"Ka cancanci bankwana mai kyau saboda matsayinka: ɗaya daga cikin ƴan wasa masu muhimmanci a tarihin ƙungiyar, ba a kore ka ba da matsayinka. Amma gaskiyar ita ce a yanzu ba abin mamaki ba ne," kamar yadda Messi ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Komin runtsi, sabon kocin Barcelona Ronald Koeman har yanzu ba shi da wani zaɓi illa ƙoƙarin daidaita ƙungiyar da kuma sake gina ta da ɗan wasan na Argentina, wanda halayensa da wuya su canza waɗanda kuma za a ci gaba da sharhi akai a makwanni masu zuwa.

Messi yana da damar komawa wata ƙungiya a watan Janairu, don haka Koeman ba ya da lokaci mai yawa da zai sauya ra'ayin kaftin ɗin bisa niyya sake gina tawagar tare da shi.

Idan har kocin ya gagara sauya ra'ayin Messi, matsalar za ta ci gaba da yin muni.

Wa zai buga lamba 9?

Barin Suarez ya tafi wata alama ce musamman da shugaban Barcelona Bartomeu ke son kawar da waɗanda shekarunsu suka ja a tawagar da Bayern Munich ta wulaƙanta a gasar zakarun Turai.

Amma kuma wani abu ne daban: ƙungiyar ba ta da kuɗi - amincewa da buƙatar Wolves kan Nelson Semedo duk da a baya Bartomeu ya ce ba na sayarwa ba ne - da kuma tafiyar Suarez wani mataki ne na samun kuɗi.

Sannan hakan ya bar giɓin wa zai zama a gaba. Duk da akwai zubin ƴan wasa kamar Messi da Antoine Griezmann da Philippe Coutinho da Ousmane Dembele da kuma matasan ƴan wasan gaba Ansu Fati da Trincao.

Amma baya ga Martin Braithwaite da ke jinya, babu wani wanda za a bayyana a matsayin cikakken lamba 9.

Ana tunanin Koeman zai dinga saka Messi a gaba, amma ɗan wasan na Argentina dole zai dinga sauka a wuraren su Griezmann da Coutinho suke bugawa - dalili ɗaya da ya hana su taka wata rawar gani.

Don haka kocin yana da babban aiki na sauya tsarin ƙungiyar wanda zai ba ƴan wasansa damar aiki da kyau kuma a tare.

Idan har Koeman ya yi maganin wannan matsalar, sakamakon zai kasance mai kyau. Amma hakan za ta faru?

Ina ƴan wasan baya?

Wulakancin ci 8-2 da Bayern Munich ta yi wa Barcelona ya nuna cewa Barca tana da matsala a baya, amma ya nuna cewa Koeman ba zai iya magance matsalar ba.

Ficewar Semedo ya nuna ɗan wasan baya a gefen dama ɗaya ne yanzu Barcelona take da shi wato Sergi Roberto, wanda asalinsa ɗan wasan tsakiya ne.

A ɗayan ɓangaren kuma Jordi Alba mai shekara 31, shi ne zaɓin da ya rage wa Barcelona a gefen hagu a baya duk da ya rage yin wasa kamar a shekaru biyu da suka gabata, yayin da kuma burin Barcelona na sayan Samuel Umtiti babbar barazana ce ga makomar bayan Barcelona.

Barcelona na son ɗauko sabbin ƴan wasa musamman ɗan wasan Ajax, Sergino Dest da ɗan wasan Norwich, Max Aarons da kuma Eric Garcia na Manchester City. Amma rashin ƙudin da Barcelona ke fama da shi ya nuna da wahala a ga sabbin fuska a tawagar.

Wata matsalar kuma ita ce gola Marc-Andre ter Stegen, wanda ke ceton ƙungiyar a lokuta da dama, a yanzu yana jinya har zuwa Nuwamba.

Ko Koeman zai iya saita abubuwa?

Duk da zubin fitattu da ingantattun ƴan wasa, amma taɓarɓarewar tawagar ta dogara ne da rashin daidaito a fasalinsu gaba ɗaya.

Babbar tazara tsakanin ƴan wasan gaba da baya, shi ke ba ƴan wasan tsakiya wahala musamman wajen kare wani mugun hari. Wannan gazawar ce ta fito fili a kashin da Bayern ta ba Barcelona, kuma haka aka gani a La Liga, inda aka fi zirara wa Barcelona ƙwallaye 13 a raga fiye da Real Madrid a kakar da ta gabata.

Ana tunanin Koeman zai yi amfani da tsarin 4-2-3-1 , ta hanyar haɗa Frenkie de Jong da Sergio Busquets ko sabon ɗan wasa Miralem Pjanic a tsakiya.

Za a iya tilasta kawo ƙarshen shugabancin Bartomeu?

Wani abin da zai shafe komi shi ne makomar shugaban Barcelona Bartomeu, wanda ke fuskantar barazanar ƙuri'ar yankan ƙauna inda sama da mambobin ƙungiyar 20,000 suka sanya hannu na adawa da shi.

A watan Maris ne wa'adin Bartomeu zai kawo ƙarshe amma masu adawa da shi na son ya tafi cikin gaggawa tun kafin cikar wa'adin - ƙila hakan nufin kwantar da hankalin Messi da kuma janyo ra'ayinsa ya ci gaba da taka leda a kulub ɗin.

Babban ƙarfin Barcelona - kulub ɗin ya kasance na mambobi 140,000 - shin ko magoya baya za su iya yin tasiri na gaske kan harakokin tafiyar da ƙungiyar (misali a ce idan magoya bayan Manchester United za su iya tilasta korar masu kulub din ƴan gidan Glazer kamar yadda ake son korar Bartomeu daga Camp Nou).