Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rice, Rudiger, Skriniar, Smalling, Kounde, Aouar, Arrizabalaga
KocinChelsea Frank Lampard yana so Stamford Bridge ta dauko dan wasan West Ham mai shekara 21 Declan Rice. Sai dai da zarar kungiyar ta dauko Rice, dan wasan Italiya Jorginho zai tafi Arsenal, a cewar(Mirror).
Kazalika Lampard yana shirin tattaunawa da golan Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, bayan dauko golan Senegal Edoaurd Mendy, mai shekara 28. (Star)
Paris St-Germain na son sayo dan wasan Chelsea Antonio Rudiger amma tana jira ta gani ko za a bari wata kungiyar ta karbo aro ko ma ta sayi dan wasan na Jamus mai shekara 27. (Telegraph - subscription required)
Tottenham na tattaunawa da zummar dauko dan wasan Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25 - sai dai ba za ta bari a tilasta mata biyan farashin £55m da Inter Milan ta sanya kan dan wasan ba. (Sun)
Inter za ta nemi dauko dan wasan Manchester United da Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, idan suka sayar wa Tottenham Skriniar. (Football Italia)
Sevilla tana sa ran Manchester City za ta sake taya dan wasanta Jules Kounde kuma da wahala ta ki amincewa da tayin City idan kudin da za ta biya sun kai tsakanin euro 65-70m kan dan wasan na Faransa mai shekara 21. (ESPN)
Arsenal ta mika £32m don sayo dan wasan Lyon Houssem Aouar, mai shekara 22, amma kungiyar da ke buga Ligue 1 tana so a biya ta £54m kafin ta saki dan wasan na Faransa. (RMC Sport, via Metro)
Aouar ya amince ya tafi Arsenal bayan Manchester City da Juventus sun ki taya shi. (Telefoot, via Mirror)
Dan wasan Liverpool da Ingila Rhian Brewster, mai shekara 20, yana so ya tafi Sheffield United, duk da sha'awar da Aston Villa da Brightonsuke yi na daukarsa.(Sheffield Star)